FCTA za ta rushe wasu gidajen rawa 2 saboda karya dokar COVID-19
- Hukumar Babban Birnin Tarayya ta yi alwashin rusa wasu gidajen rawa biyu a Abuja
- Hukumar ta bayyana cewa an kama gidajen rawan da karya doka da ka'idojin Korona
- Hukumar ta kuma bada wasu ka'idoji da zasu iya hana rusa gidajen rawan guda biyu
Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta lashi takobin rusa gidajen rawa na dare guda biyu a garin Karu da ke kewayen birni a cikin karamar Abuja Municipal Area Council (AMAC) saboda keta dokokin ladabi na COVID-19.
An garkame gidajen rawan Cool Leo da Paris dake Karu a ƙarshen mako saboda ƙeta ka'idojin COVID-19 da kuma dokokin gudanar da kasuwanci da gwamnati ta shata, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban wayar da kan Jama'a na rundunar ta FCTA Task Force akan Tilasta bin ka'idojin COVOD-19, Ikharo Attah, ya bayyana hakan a dandalin Eagle Square yayin shari'ar mutane 29 da aka kama a fadin FCT saboda karya ka'idojin COVID-19.
KU KARANTA: A baiwa 'yan Najeriya damar mallakar bindiga, in ji kungiyar miyetti Allah
Com Attah ya ce hukumomi ba za su tsaya komai ba don tabbatar da rusa mashahuran gidajen rawan guda biyu sai dai idan sun koma ga amfani da filayen zama na yankin.
Ya bayyana cewa, “An nemi gidajen rawan guda biyu da ke Karu su rufe. Suna aiki a wuraren zama ba tare da bin ladabin COVID-19 ba kuma suna lalata zaman lafiyar mazauna cikin dare. Su ne Paris Club da Cool Lea kuma an kulle su ba ranar budewa.
“Idan suka ki komawa, to sai mu kira wasu bangarorin na Babban Birnin Tarayya ta rusa su. Ba za mu ba su damar ci gaba da hargitsa unguwar ba.”
KU KARANTA: Buhari yana kokarin gyara matsalolin Najeriya, in ji Amb Yabo
A wani labarin, Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya fadawa shugabannin kasashen Afirka da su kalli annobar COVID-19 a matsayin tursasawa ba cikas ga cikakken aiwatar da yankin Kasuwancin Kasashen Afirka (AfCFTA) ba.
Obasanjo ya ce jinkirin cikakken aiwatarwa sakamakon barkewar annobar ya kamata ya ba shugabanni “damar yin karin aiki tukuru wanda ke bukatar dan lokaci ta yadda idan daga karshe za mu fara aiki mu kasance cikin shiri da kuma yin hakan a cikakken karfi.”
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng