Nasara daga Allah: Sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram 81 a Sambisa

Nasara daga Allah: Sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram 81 a Sambisa

- Sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka mayakan Boko Haram 81 a dajin Sambisa

- Sai dai, 'yan ta'addan sun hallaka soja daya a wani harin nakiya da suka harba kan sojojin

- Rundunar sojojin ta kuma fatattaki wasu daga cikin 'yan ta'addan da dama zuwa dajin

Sojojin Najeriya sun samu kashe mayaƙan Boko Haram 81 a dajin Sambisa. Sai dai sun rasa soja daya a wani harin nakiya, BBC Hausa ta ruwaito.

Kafar yaɗa labarai ta PRNigeria ta ruwaito cewa a yayin tserewa mayaƙan sun lalata gidaje tare da kona wasu.

Sojojin dai sun tarwatsa ƙauyukan ƴan ta'addar da damma a yankin garin Bello da Kwoche da Lawanti da Alfa Bula Hassan da Alfa Cross da dai sauransu.

KU KARANTA: Osinbajo yayi Allah wadai da harin da ake kaiwa yan Arewa a Shasha

Nasara daga Allah: Sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram 81 a Sambisa
Nasara daga Allah: Sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram 81 a Sambisa Hoto: TRT World
Source: UGC

PR Nigeria ta ce wata majiyar leken asiri ta ce sojojin sun gamu da tirjiyar mayaƙan na Boko Haram wadanda suka ajijiye abubuwan fashewa a hanyar da dakarun Najeriyar ke bi.

Kuma a nan ne soja daya ya rasa ransa, hudu suka samu manyan raunuka.

Babban hafsan soji Mejo Janar Ibrahim Attahiru ya yabi sojojin bisa jumurinsu da ƙwazonsu kuma ya buƙaci su ci gaba da jurewa.

A wani ɓangaren kuma, PRNigeria ta ruwaito cewa wasu mayakan Boko Haram da ke tserewa sun afka wa ƙauyukan Zira da Gur a ƙaramar hukumar Biu ta Kudu a jihar ta Borno.

Mayaƙan sun shiga garuruwan ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin Lahadi a kan babura da motocin yaƙi sannan sun kona gidaje da dama yayin da mazauna ƙauyukan suka tsere.

Jirgin yakin rundunar saman Najeriya sun fatattaki ƴan bindigar daga sama.

KU KARANTA: FCTA za ta rushe wasu gidajen rawa 2 saboda karya dokar COVID-19

A wani labarin, Gwamnatin tarayya ta bukaci gwamnonin Jihohi da sauran wakilai da su ba da tasu gudummawar wajen magance ‘yan fashi da sauran matsalolin tsaro da ke addabar al’ummar kasar, Daily Trust ta ruwaito.

Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (Rtd) ya ba da wannan furucin a ranar Asabar a Kano bayan ya sake jaddada rajistarsa na jam’iyyar APC a shiyyarsa ta Galadanchi da ke ƙaramar hukumar Gwale ta Jihar Kano.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel