Valentine: Tsohon Gwamna ya mamayi Mai dakinsa a gida a ranar Masoya ta Duniya

Valentine: Tsohon Gwamna ya mamayi Mai dakinsa a gida a ranar Masoya ta Duniya

- Rochas O. Okorocha ya yi bikin Valentine da mai dakinsa, Nneoma Nkecho Okorocha

- Sanatan ya shafe shekara da shekaru ya na auren Madam Nneoma Nkecho Okorocha

- Sanata ya saya wa Nneoma Okorocha kayan jin dadi domin tuna ranar Valentine jiya

Sanata Rochas Owelle Okorocha ya shiga sahun wadanda su ke yin bikin ranar masoya ta Duniya watau Valentine a rana irin ta jiya, 14 ga watan Fubrairu.

Tsohon gwamnan Imo, Rochas Owelle Okorocha da mai dakinsa, Nneoma Nkecho Okorocha su na cikin miliyoyin mutanen da aka yi wannan biki da su a jiya.

‘Dan siyasar ya ba sahibarsa mamaki, ya yi mata kyaututtuka domin nuna soyayyar da ke tsakaninsu a rana da masoyan Duniya ke sabunta kaunarsu.

Kamar yadda wani bidiyo ya nuna, Rochas Okorocha ya dauki uwargidar ta sa zuwa wani daki a gidansu, inda ya nuna mata wasu tulin kaya da ya saya mata.

KU KARANTA: Matasan da gidauniyar Kwankwasiyya ta aika karatu, sun fara dawowa

Kawo yanzu wannan bidiyo ya na ta yawo a shafin Instagram, inda aka ga Sanatan na APC ya na ba mai dakinsa kyaututtuka, sannan ya yi wani gajeren jawabi.

Wasu ‘yanuwa da abokan arziki su na gidan Rochas Okorocha lokacin da aka yi wannan, su ka shaida irin soyayyar da ke tsakanin wadannan ma’auratan.

A bidiyon, za a ga Sanatan na yammacin Imo mai shekara 58 ya na sunbantar uwargidarsa a daki.

Sanata Okorocha ya dade tare da Nneoma Nkecho Okorocha, kuma har ta haifa masa ‘ya ‘ya shida: Uloma Nwosu, Uju Okorocha, da Uchechi Rochas Okorocha.

KU KARANTA: Za a tafka asarar inna-naha a dalilin haramta mu’amalar Cryptocurrency

Valentine: Tsohon Gwamna ya mamayi Mai dakinsa a gida a ranar Masoya ta Duniya
Tsohon Gwamnan Imo da matarsa Hoto: Instagram
Asali: Instagram

Ragowar ‘ya ‘yansu maza su ne: Ahamefula Brendan, Amarachi Rochas da Amen Rochas.

Dazu ne da safen nan mu ka samu labari cewa Ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika ya rasa shugaban ma'aikatan ofishinsa, Malam Ibrahim Idris.

A safiyar Litinin, 15 ga watan Fabrairun 2021 ne ma'aikatar sufurin jiragen saman ta sanar da wannan lamarin, ta na cike da alhini da dimuwa a shafin Twitter.

Sanarwar ta ce: "Mutum mai matukar kokari, tsoron Allah da saukin kai. Allah ya yafe masa ya kuma saka shi a Aljannah."

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng