Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya rasa shugaban ma'aikatansa

Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya rasa shugaban ma'aikatansa

- Ibrahim Idris, fitaccen shugaban ma'aikatan ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya rasu

- Idris wanda yake shugabantar ma'aikatan ministan sufuri ya rasu a daren Lahadi, 14 ga watan Fabrairu

- Ma'aikatar sufurin jiragen sama ta tarayya ce ta sanar da rasuwar idris a safiyar Litinin, 15 ga watan Fabrairu

Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya rasa shugaban ma'aikatansa, Ibrahim Idris a daren Lahadi, 14 ga watan Fabrairun 2021.

A safiyar Litinin, 15 ga watan Fabrairun 2021 ne ma'aikatar sufurin jiragen saman ta sanar da wannan lamarin mai cike da alhini da dimuwa a shafinta na Twitter.

KU KARANTA: Za a iya samun kwanciyar hankali bayan rabuwa, zubar da kiyayya ake yi, Rahama Indimi

Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya rasa shugaban ma'aikatansa
Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya rasa shugaban ma'aikatansa. Hoto daga @fmaviationng
Asali: Twitter

Kamar yadda ma'aikatar ta wallafa a shafinta na Twitter: "Daga Allah muke, gare shi za mu koma. Tare da fawwalawa Allah dukkan lamurra muke sanar da rasuwar Dr. Ibrahim Idris, shugaban ma'aikatan mai girma Hadi Sirika a daren jiya.

"Mutum mai matukar kokari, tsoron Allah da saukin kai. Allah ya yafe masa ya kuma saka shi a Aljannah."

Sirika, ministan sufurin jiragen sama ya yi martani a kan rashin shugaban ma'aikatansa da yayi a shafinsa na Twitter.

Ya kwatanta mamacin da mutum mai gaskiya da rikon amana wanda yayi rayuwa mai kyau tare da mu'amala mai kyau da jama'a.

KU KARANTA: Za mu yi ramuwar gayya idan aka hana makiyaya zaman kudu, Kungiyar Fulani

A wani labari na daban, dakarun sojin Najeriya sun halaka gagararrun kwamandoji biyu na Boko Haram, Abul-Bas da Ibn Habib a Banki, kusa da Pulka a jihar Borno kamar yadda PM News ta wallafa.

Kamar yadda aka gano, kwamandojin biyu tare da masu tsaronsu da mayaka duk an kashe su a ranar Juma'a bayan sojin Najeriya sun kai musu hari.

Abul-Bas da Ibn Habib na daga cikin manyan kwamandojin Boko Haram amma na bangaren Shekau wadanda ke ta'adi a dajin Sambisa da kewaye.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel