Kwankwasiyya: An bada gudumuwar kudi domin karatun Talakawa 370
A jiya 29 ga Watan Yuni, 2019 ne kungiyar cigaban al’ummar nan ta Kwankwasiyya Foundation ta shirya bikin karbar gudumuwar kudi domin aika wasu yaran jihar Kano zuwa jami’o’i na kasar waje.
Idan ba ku manta ba tun kwanakin baya ku ka ji shelar tura yara 370 domin su yi Digiri na Masters a kasashen ketare. Kungiyar Kwankwasiyya Foundation a karkashin tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso ta shirya wannan.
Sanata Rabiu Kwankwaso da dinbin manyan mutane sun halarci wannan biki. A taron da a ka yi jiya, manyan ‘yan kasuwa irin su Alhaji A.A Rano mai kamfanin mai a Najeriya ya bada gudumuwar Naira miliyan 30.
KU KARANTA: Kwankwaso zai saida kadarorinsa domin Talaka ya je Makaranta
Haka zalika wani Takwaransa a harkar dukiya, Alhaji Abdussamad Isiyaka Rabiu ya bada kudi Naira miliyan 20. Injiniya Sagir Koki, ya cire Naira miliyan 5 daga aljihunsa ya ba wannan gidauniya domin ilmantar da yara.
Malam Ibrahin Adam, wani daga cikin Hadiman ‘dan takarar gwamnan jihar Kano a PDP, Abba Yusuf, ya bayyana wannan a shafin sa na Tuwita. A cewar sa, yanzu an samu kudin da su ka kai N87, 727, 000 a asusun gidauniyar.
An samu sauran mutane da dama da su bada na su gudumuwar, daga ciki har da manyan ‘yan siyasa na Kwankwasiyya da Matasa da sauran gama-gari. Hazikan Matasa fiye da 300 a ka zaba domin a tura su karatu a kasar waje.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng