Rashawa ce ta saka na yi murabus daga NDDC – Kwankwaso

Rashawa ce ta saka na yi murabus daga NDDC – Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, a ranar Asabar ya ce ya yi murabus ne daga Hukumar Cigaban Niger Delta, NDDC, a 2010 saboda rashawar da ya gani a hukumomin gwamnati barkatai.

Ya ce hakan ya faru ne sakamakon gazawar shugabannin waɗannan hukumomin.

Kwankwaso, tsohon mai neman takarar shugabancin ƙasa ya yi murabus daga naɗin da aka yi masa a kwamitin zartarwa na hukumar a shekarar 2010.

Kwankwaso ya kuma ce ya ajiye mukaminsa a hukumar saboda irin rashawar da ya ga ana tafkawa a hukumar "da shi kuma baya ya son ayi da shi".

Rashawa ce ta saka na yi murabus daga NDDC – Kwankwaso
Rashawa ce ta saka na yi murabus daga NDDC – Kwankwaso. Hoto daga Pulse Ng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kashe shugaban ƴan bindiga ‘Dangote’ yayin sumamen da sojoji suka kai a Zamfara (Bidiyo)

Tsohon gwamnan ya shaidawa BBC Hausa cewa "haɗama da neman tara dukiya irin ta ma'aikatan gwamnati" ne sanadin rashawa a hukumar ta NDDC.

A baya, an taba zargin Kwankwaso da tafka rashawa shi kansa.

Daily Trust ta ruwaito yadda aka rubuta takardar korafi ga Hukumar Yaki da Rashawa ta EFCC a in tsohon gwamnan inda ake zargin ya wawure Naira biliyan 3.8 na zaben ƙananan hukumomi yayin zaɓen 2015.

Ƙorafin da ake aike a kan Kwankwason ta kuma yi iƙirarin ya tilasta wa Shugabannin ƙananan hukumomi 44 na Kano su bayar da N70m kowannensu don takarar shugabancin ƙasar da zai yi.

Amma Kwankwaso ya musanta dukkan waɗannan zargin da ake masa.

A shekarar 2020, an zargi shi da magajinsa Gwamna Abdullahi Ganduje da hannu cikin handame kuɗin kwangilar tsaro, N35 biliyan, amma ya musanta wannan zargin.

A hirar da aka yi da shi a ranar Asabar, Kwankwaso ya ce baya ƙaunar rashawa kuma ba zai taɓa yarda ya shiga harkar ba.

"Lokuta da dama, ba a ɗaukan mataki a kan mutanen da ke yi wa tattalin arziki zagon ƙasa ta hanyar sata daga baya ma su ke shiga gwamnatin.

"Abinda ya faru a NDDC sakacin shugabanni ne. Idan shugabanni suna sa ido kan maƙuden kuɗaɗen da ake basu ko kuma bashi, da hakan bai faru ba," in ji tsohon gwamnan.

Da aka tambaye shi dalilin da yasa bai tona rashawar da ke faruwa a NDDC ba, ya ce, "rashawar ta ƙazanta ne".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164