Miyetti Allah ta bada sharuddan dakatar da rikici tsakanin manoma da makiyaya

Miyetti Allah ta bada sharuddan dakatar da rikici tsakanin manoma da makiyaya

- Kamar yadda ya zama abin magana a Najeriya, Fulani da Makiyaya suna ta rikici kan wasu dalilai

- Kungiyar Fulani ta miyetti Allah ta bayyana hanyoyin da gwamnati za ta bi don magance rikici

- Kungiyar ta bayyana goyon bayanta kan daukar matakan horarwa ga makiyaya a yankin kudu

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), a Kudu maso Gabas, ta ce za ta goyi bayan duk wata manufa ta gwamnati da ke neman dakatar da rikici tsakanin al'ummomin da ke yankin da makiyaya.

Ta lissafa wasu sharudda da gwamnati za ta bi don dakatar da rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin mambobinta da manoma a kasar, The Nation ta ruwaito.

Shugaban kungiyar a yankin kudancin Najeriya ya bayyana amincewar kungiyar kan kudurin horar da makiyayan kiwon a zamanance.

KU KARANTA: Mutane da dama sun mutu a rikicin Hausawa da Yarbawa a jihar Oyo

Miyetti Allah ta bada sharuddan dakatar da rikici tsakanin manoma da makiyaya
Miyetti Allah ta bada sharuddan dakatar da rikici tsakanin manoma da makiyaya Hoto: The Sun News
Source: UGC

A cewar Siddiki, "matsayar gwamnan ci gaba ne abin maraba, amma don manufar ta yi aiki kamar yadda ake fata, dole ne a samar da wadannan tanade-tanade don zaman lafiya da daidaito.

“Suna horarwa tare da sake horar da Fulani makiyaya kan sana'ar kiwo na zamani, samar da filin kiwo a jihohi 36 na tarayya da babban birnin tarayya da kuma ci gaba da Taron Tattaunawa na gari tsakanin Gwamnati, Manoma da Makiyaya a yankunan da abin ya shafa.

Siddiki ya kara da cewa, "Na yi imani da wadannan, zasu kawo karshen rikicin da ke tsakanin manoma da makiyaya a kasar."

Kungiyar ta ci gaba da cewa mafi yawan mambobinta ba su da ilimin yin kiwo a zamanance yayin da suke kira ga gwamnati da ta shirya horo kan hakan ga masu kiwo.

Da yake magana da manema labarai ranar Asabar a Awka, Jihar Anambra, Shugaban kungiyar a yankin Kudu maso Gabas, Alhaji Gidado Sidikki, ya ce kusan 89% na makiyaya ba su da ilimin kiwo na zamani.

"Ya kamata gwamnati ta horar da mu ta yadda za mu iya tafiya da tsarin zamani na kiwon dabbobi domin yawancinmu ba mu da ilimin Noma na Fasaha."

KU KARANTA: Gwamnatin Saudiyya ta rufe wasu masallatai saboda saba dokar Korona

A wani labarin, Sakamakon umarnin fatattakar makiyaya masu aikata laifuka a wasu jihohin kudu, kimanin makiyaya 4,000 sun bar jihohin kudu zuwa Kaduna, Nigerian Tribune ta ruwaito.

An tattaro cewa makiyayan tun makon da ya gabata suna dawowa zuwa garin Labduga, karamar hukumar Kachia, jihar Kaduna.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel