Disamba 2020: Kason da kowani bangare ya kwashe daga N601.11bn na kudaden da FG ke rabawa duk wata

Disamba 2020: Kason da kowani bangare ya kwashe daga N601.11bn na kudaden da FG ke rabawa duk wata

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) a ranar Alhamis, 11 ga watan Fabrairu, ta fitar da rahoton yadda aka kasafta kudin Disamba 2020 na kudin wata-wata da ake rarrabbawa daga asusun gwamnatin tarayya (FAAC).

A cewar NBS, FAAC ta raba kudi naira biliyan 601.11 a tsakanin bangarorin uku na gwamnati, wato gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi, a watan Disambar 2020 daga kudaden shigar da aka samu a watan Nuwamba 2020.

A wannan zauren, Legit.ng ta kawo muku yawan kudin da gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi suka samu da kuma sauran muhimman bayanai.

Disamba 2020: Kason da kowani bangare ya kwashe daga N601.11bn na kudaden da FG ke rabawa duk wata
Disamba 2020: Kason da kowani bangare ya kwashe daga N601.11bn na kudaden da FG ke rabawa duk wata Hoto: Femi Adesina
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: 2023: PDP za ta sha mummunan kaye a Zamfara, cewar jigon APC

Tushen kudaden da aka rarraba

1. An ciro N436.46bn daga asusun dokar ajiyar kudade na gwamnati

2. N7.87bn ta fito daga asusun hada hadar kudade na FOREX

3. Sai kuma N156.79bn daga harajin da ake cirewa daga kayayyaki (VAT)

Adadin kudin da gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi suka raba

1. Gwamnatin Tarayya - N215.60bn

2. Jihohi - N171.17bn

3. Kananan hukumomi - N126.79bn

4. An raba kashi 13 cikin 100 na ribar da kasa ta samu daga sayar da man fetur a tsakanin jihohin da ke samar da mai - N31.39bn

Hukumomin da ke samar da kudaden shiga

Legit.ng ta tattaro cewa hukumomin sun tattara kudin a matsayin kudaden shiga.

1. Hukumar Kwastan ta Najeriya (NCS) - N7.87bn

2. Hukumar tattara kudaden shiga ta tarayya (FIRS) - N9.41bn

3. Ma'aikatar Albarkatun Man Fetur (DPR) - N3.98bn

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Arewa na zargin dattawan Yarbawa da kokarin haifar da tsoro da tashin hankali

Jihohi

1. FCT - N2,636,349,331.05

2. Abia - N2,725,573,706.34 (da karin 13% na man fetur)

3. Adamawa - N2,533,228,542.88

4. Akwa Ibom - N9,525,021,262.99 (da karin 13% na man fetur)

5. Anambra - N2,528,482,837.44

6. Bauchi - N3,041,849,567.55

7. Bayelsa - N7,305,875,525.84 (da karin 13% na man fetur)

8. Benue - N2,851,930,607.00

9. Borno - N3,159,530,390.93

10. Kuros Riba - N2,557,205,671.63

11. Delta - N12,391,554,363.96 (da karin 13% na man fetur)

12. Ebonyi - N2,275,087,173.77

13. Edo - N3,388,632,115.37 (da karin 13% na man fetur)

14. Ekiti - N2,273,803,355.34

15. Enugu - N2,557,426,375.75

16. Gombe - N2,395,310,672.48

17. Imo - N3,328,199,887.28 (da karin 13% na man fetur)

18. Jigawa - N2,843,869,791.00

19. Kaduna - N3,331,924,231.91

20. Kano - N4,033,665,225.44

21. Katsina - N3,125,975,751.80

22. Kebbi - N2,685,228,766.44

23. Kogi - N2,810,623,873.67

24. Kwara - N2,263,665,861.23

25. Lagos - N3,406,691,958.53

26. Nasarawa - N2,345,162,696.29

27. Neja - N3,012,257,067.32

28. Ogun - N2,362,580,223.78

29. Ondo - N3,118,015,835.51 (da karin 13% na man fetur)

30. Osun - N2,319,269,432.22

31. Oyo - N 2,852,245,711.37

32. Plateau - N2,655,534,749.87

33. Koguna - N8,143,229,804.88 (da karin 13% na man fetur)

34. Sokoto - N2,802,625,918.64

35. Taraba - N2,449,612,149.17

36. Yobe - N2,525,235,670.34

37. Zamfara - N2,530,613,684.96

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel