Majalisar Dattawa ta gayyaci Gwamnan CBN yayi bayani kan haramta Bitcoin

Majalisar Dattawa ta gayyaci Gwamnan CBN yayi bayani kan haramta Bitcoin

- Majalisar dattawa ta gayyaci masu ruwa da tsaki kan harkar kudade a Najeriya kan kudin intanet

- Majalisar, ta gayyaci har da gwamnan Babban Bankin Najeriya don bada bayanin kan haramta kudin

- Majalisar ta bayyana cewa ya kamata a zauna a fayyace menene usulubin haramta kudaden intanet din

Majalisar dattijai, a ranar Alhamis, ta umarci kwamitinta na Banki, Inshora da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi, da su gayyaci Gwamnan Babban Bankin, Godwin Emefiele da Darakta-Janar na Hukumar Tsaro da Musayar Lamido Yuguda, don tattaunawa kan kudin intanet.

Don tattauanawa da Kwamitin Banki da Kudin da Sanata Uba Sani ke jagoranta ana gayyatar Kwamitocin Fasahar Sadarwa da Sadarwa da Cin Hanci da Rashawa da Kasuwar Hannun Jari, tare da Sanata Yakubu Oseni da Ibikunle Amosun a matsayin shugabanni.

Kudurin ya biyo bayan umarnin CBN na dakatar da cibiyoyin kuɗi daga yin ma'amala da kudaden intanet, Nigerian Tribune ta ruwaito.

KU KARANTA: Makiyaya 4,000 sun yi hijra daga jihohin kudu zuwa jihar Kaduna

Majalisar Dattawa ta gayyaci Gwamnan CBN kan haramta kudin intanet
Majalisar Dattawa ta gayyaci Gwamnan CBN kan haramta kudin intanet Hoto: Sundiata Post
Asali: UGC

Babban Bankin Najeriya ya bayyana hanin a matsayin yunkuri na kare 'yan kasar.

Da yake daukar nauyin gabatar da kudirin, Sanata Dung Gyang, mai wakiltar Filato ta Arewa ya ce matakin umarnin na CBN ya jawo martani daga 'yan Najeriya kuma ya zama batun cece-kuce a kasar baki daya.

"Babban bankin na CBN zai kasance mai bada bayani kuma kwamitin zai gabatar da rahoto ga majalisar dattijai, don majalisar dattijan ta kasance a kan kyakkyawan jagoranci kan matsayin da ya dace a kan wannan lamarin."

Sanata mai wakiltar Lagos ta yamma kuma mai goyon bayan gayyatar, Adetokumbo Abiru ya ce ya kamata babban bankin ya kara yin bincike don samun isassun bayanai kan yawan aikin da ake yi na tsarin cryptocurrency a kasar.

KU KARANTA: Filayen jirgin saman Najeriya suna daga cikin masu muni a duniya, in ji wata hukuma

A wani labarin, Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Dokta Isa Pantami a ranar Laraba ya ce Gwamnatin Tarayya za ta sanar da lokaci ga 'yan Nijeriya don hade Lambobin Shaida na Kasa (NINs) da asusun banki, The Nation ta ruwaito.

Pantami, wanda ya zanta da manema labarai na gidan gwamnati a karshen taron Majalisar zartarwa ta Tarayya (FEC), ya ce nan ba da jimawa ba za a fitar da jadawalin yadda za a hada NIN da asusun banki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.