Kungiyar Arewa na zargin dattawan Yarbawa da kokarin haifar da tsoro da tashin hankali

Kungiyar Arewa na zargin dattawan Yarbawa da kokarin haifar da tsoro da tashin hankali

- An zargi dattawan Yarbawa da mayar da hankali wajen tayar da rikici tsakanin ‘yan Najeriya

- Shahararriyar kungiyar dattawan arewacin Najeriya ce ta yi wannan zargi

- Kungiyar ta yi bayanin cewa wasu labaran da yan Najeriya da zababbun shugabanni ke yadawa suna haifar da tsoro

Biyo bayan hauhawar matsalolin tsaro a kasar, Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) a ranar Juma’a, 12 ga watan Fabrairu, ta zargi wasu dattawan Yarbawa da kokarin tayar da rikici da haifar da fargaba a tsakanin mutane.

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa kungiyar wacce ta yi zargin a wata wasika da ta rubuta wa Majalisar Dinkin Duniya ta lura cewa an yi hakan ne don haifar da rikici a tsakanin kungiyoyi da yankuna.

KU KARANTA KUMA: 2023: PDP za ta sha mummunan kaye a Zamfara, cewar jigon APC

Kungiyar Arewa na zargin dattawan Yarbawa da kokarin haifar da tsoro da tashin hankali
Kungiyar Arewa na zargin dattawan Yarbawa da kokarin haifar da tsoro da tashin hankali Hoto: @GuardianNigeria
Asali: Twitter

Dr. Hakeem Baba-Ahmed, kakakin kungiyar NEF, ya bayyana cewa Najeriya na fuskantar barazana daga mutane, suna kamun kafa da kasashen duniya, don haifar da rikici a cikin kasar.

A cewar NEF, wasu labarai da barazanar da wasu zababbun jami'ai da 'yan Najeriya ke yi na kara haifar da fargabar da za ta iya hada yan kasar juyawa junansu baya cikin sauki.

Kungiyar ta kuma ba Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnoni shawara a kan daukar matakan da za su rage tashin hankali.

KU KARANTA KUMA: Kona coci da sansanin sojoji a Nigeria: Ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin kai hari

A wani labarin, kungiyar Gwamnonin Najeriya a ranar Alhamis ta yi ittafaki kan "bukatar samar da sabbin hanyoyin kiwon shanu domin maye gurbin kiwo a fili, da dare da kuma kiwon shanun da kananan yara ke yi a fadin tarayya."

A takardar da kungiyar ta saki bayan zamanta na 25 kuma shugabanta, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya rattafa hannu, gwamnonin sun yi shawaran "samar da hanyoyin aiwatar da shirin da kwamitin sauya salon kiwo a fadin tarayya ta kawo."

Gwamnonin sun yi ittifakin magance matsalar rashin tsaro wanda ke da nasaba da Makiyaya masu aikata na'ukan laifuka daban-daban, Channel TV ta ruwaito.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel