Aikata masha'a: Miji na bai ƙyale matan aure ba ballanta ƴan mata, matar fasto ta faɗa wa kotu

Aikata masha'a: Miji na bai ƙyale matan aure ba ballanta ƴan mata, matar fasto ta faɗa wa kotu

- Wani fasto ya garzaya kotu yana rokon kotu ta raba aurensa da matarsa bayan ya zarge ta da yunkurin kashe shi

- A nata bangaren matar ta bayyanawa kotun cewa mijin nata yana bin matan banza ne, inda ta ce yana kwanciya da mata mambobin cocinsa

- Kotu ta ɗage sauraren karar zuwa 19 ga watan sabuwar shekara don yanke hukunci bayan matar ta roki da kar a raba auren

Wata mata mai mai aikin da'awah yaɗa addinin Kirista, Chinwe, ta yi watsi da ƙarar saki da aka kawo akanta a kotun gargajiya da ke zamanta a Igando Legas.

Ta kuma zargi mijinta Paul Ekwe, wanda fasto ne da aikita aikin assha da mata mambobin cocinsa kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Miji na bai ƙyale matan aure ba ballanta ƴan mata, matar fasto ta faɗa wa kotu
Miji na bai ƙyale matan aure ba ballanta ƴan mata, matar fasto ta faɗa wa kotu. Hoto daga @thecableng
Asali: UGC

Faston, wanda ya shigar da ƙara gaban kotun yana roƙon ta datse igiyar auren da ke tsakaninsu da matarsa Chinwe, ya zargeta da ƙulla makirci don ganin bayansa.

DUBA WANNAN: GSS Ƙanƙara: Masu garkuwa sun ce iyayen yara su fara tanadin kuɗin fansa, sun kuma gargadi sojoji

Ya kuma zargi matarsa da sa ƴaƴansu bijire masa, inda yai zargin wai ta aurar da ɗiyarsu ɗaya ba tare da saninsa ba.

"Matata ta na shirin kashe ni saboda ta sake yin wani auren" ya faɗi hakan yana roƙon kotun da datse igiyar aurensu na tsawon shekaru 28.

Ya bayyana matarsa a matsayin fitinanniya, mai kunnen ƙashi kuma mafaɗaciya, Paul yace.

"Auren cike yake da faɗa, jayayya da ɗauki ba daɗi. Chinwe ta hana gidana da ni kaina jin daɗin rayuwa. Bata bin umarnina kuma ta na yin abin da ta ga dama son ranta."

Da take maida martani, matar tasa, Chinwe wadda ta ke da shekaru 49 ta zargi mijinta da aikita masha'a ta hanyar yin zina da mambobin cocinsu."

Matarsa ta zargi mijin nata da cin zarafi da mutuncin mata, walau mai aure ko mara aure.

Chinwe ta zargi mijinta da yi mata zanen baƙin fenti ta hanyar bayyana jama'a cewa ta na shirin ganin bayansa inda ta ce hakan kushe ne da zuƙi ta malle kurum.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Wasu da ake zargi da fashi da garkuwa sun tsere daga gidan yari

A nata bangaren, ta ce Paul ya sa yan sanda su kama ta, bisa zargin ta lalata masa coci ta kuma sace masa kimanin naira miliyan biyar.

"Ina kula dashi a zahiri da ɓoye amma duk da haka ya zabi bin mata daban daban. Har ya kawo matar aure a matsayin matarsa kuma ya kore ni daga gidansa," ta shaidawa kotu.

"Mai zan samu idan na kashe uban ƴaƴa na har bakwai; ƙarya ya ke min saboda yana son auren wata matar wanda tuni yayi.

"Miji na bashi da kula. Ina daukar duka nauyinsa amma yana kashe kudi, yana siyawa matan banza kayan abinci."

Uwar yara bakwan ta roki kotu da kada ta bawa mijin damar rabuwa da ita, ta na bayyana cewa har yanzu tana son shi duk da hallayar sa ta "bin matan banza".

Bayan sauraren bangarori biyun, Adeniyi Koledoye, shugaban kotun, ya dage sauraren karar har zuwa 19 ga watan Janairu don yanke hukunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164