2023: PDP za ta sha mummunan kaye a Zamfara, cewar jigon APC

2023: PDP za ta sha mummunan kaye a Zamfara, cewar jigon APC

- Wani jigon APC a jihar Zamfara, Aminu Jaji, ya ce jam’iyyar za ta kwato jihar a 2023

- Jaji ya jaddada cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) bata da mazauni a jihar

- Tsohon dan majalisar ya kuma bayyana cewa APC ta hade a yanzu domin tsige gwamnati mai ci a 2023

Kimanin mako guda bayan bangarorin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) biyu a Zamfara sun janye takobinsu tare da rungumar zaman lafiya, wani tsohon dan majalisar wakilai, Aminu Sani Jaji, ya yi hasashen nasarar jam'iyyar a 2023.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Jaji, wanda ya kasance tsohon shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin tsaron cikin gida kuma dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC a jihar a shekarar 2019, ya ce jam’iyyar za ta karbi ragamar mulki a 2023.

KU KARANTA KUMA: Sabunta rijistar jam'iyyar APC: Abdul'aziz Yari ya caccaki ra'ayin Tinubu

Legit.ng ta tattaro cewa Jaji ya ce ba don rashin jituwar da ya wakana a lokacin babban zaben da ya gabata ba da kuma hukuncin kotu da ta soke muradin mutane, ita kanta jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai mulki a jihar ta san cewa ba ta da mazauni a Zamfara.

2023: PDP za ta sha mummunan kaye a Zamfara, cewar jigon APC
2023: PDP za ta sha mummunan kaye a Zamfara, cewar jigon APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Jaji ya ce jam'iyyar mai mulki a jihar a cikin 'yan kwanakin nan tana fuskantar sauyin shekar mambobinta zuwa jam'iyyar APC.

Ya ce:

“Zan iya bugan kirjin cewa za mu karbe jihar Zamfara saboda maimakon mutanenmu su sauya sheka zuwa PDP, magoya bayan PDP ne ke sauya sheka zuwa APC. Don haka ka ga mun riga mun rage kuri'u 180,000 da PDP ta samu tun kafin 2023.”

KU KARANTA KUMA: Sauyin yanayi ne ke sa makiyaya daga waje shigowa Nigeria, In ji Ganduje

A wani labarin, Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce sun tattauna batun sauya sheka da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, daga jam'iyyar PDP ya koma jam'iyyar APC.

A wani bidiyo da aka daura a taron jam'iyyar APC da aka yi a jihar Kogi wanda aka saki a kafar sada zumunta ranar Laraba, Bello ya ce wannan yana daya daga cikin nasarorin da ya samu a matsayinsa na shugaban samari na kwamitin rijista da tabbatar da 'yan jam'iyya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng