Sabunta rijistar jam'iyyar APC: Abdul'aziz Yari ya caccaki ra'ayin Tinubu

Sabunta rijistar jam'iyyar APC: Abdul'aziz Yari ya caccaki ra'ayin Tinubu

- Abdulaziz Yari ya ce APC ta yanke shawarar sabunta rijistar 'ya'yanta ne bayan gano cewa an mayar rumbun bayanan rijistar Legas

- A cewar tsohon gwamnan na Zamfara ya ce tun 2018 suka gano cewa bayanan ba sa babban ofishin jam'iyyar da ke Abuja

- Ya kuma bayyana adawar da Tinubu ke yi wa shirin a matsayin rashin fahimtar manufar abun

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari ya yi tsokaci a kan manufar sabunta rijistar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ke yi wa mambobinta a fadin kasar.

A wata hira da yayi da sashin Hausa na BBC, Yari ya jaddada cewa an sabunta rijistar APC ne saboda an gano wasu sun mayar da rumbun bayanan jam'iyyar Lagos wanda hakan ya haifar da rashin gamsuwa.

KU KARANTA KUMA: Sauyin yanayi ne ke sa makiyaya daga waje shigowa Nigeria, In ji Ganduje

Sabunta rijistar jam'iyyar APC: Abdul'aziz Yari ya caccaki ra'ayin Tinubu
Sabunta rijistar jam'iyyar APC: Abdul'aziz Yari ya caccaki ra'ayin Tinubu Hoto: Nigerian Observer
Asali: UGC

Ya ce:

“Rijistar nan da aka yi akwai inda aka ajiye dandamalinta na kula da ita a tsakiya wato babban ofishin jam’iyya.

“A jam’iyya akwai wanda aka sa shi ne ke kulawa da duk abin da rumbun adana bayanan ke kulawa da ita. Amma daga karshe sai muka nema sai muka rasa a cikin zaben da aka yi na 2018. Aka ce an mayar da ita wata matattara a Lagas.

“Sai kowa ya zama ya samu rashin gamsuwa domin wadanda suke da lambobin da ake ta la’akari da gane rijista ya aka yi mutum nawa aka yi, ya al’amarin yake, sai ya zama ba su da ikon kai wa ga wadannan lambobin domin a tantance su waye ke da rijista kaza wace jiha ce take da kaza, ina ne ya kamata a kara kokari, ganin cewa a sabunta rijistar... toh duka babu wannan bayanan.

“A lokacin da su shugabannin suka zo da wannan bayanai cewa akwai bukatar a jaddada, kowa ya ba da goyon baya har sai da shi kan shi Shugaban kasa, ya aminta kuma duka mun aminta kan cewa shugabanni lallai ya kamata a jaddada wannan."

Kan batun cewa wasu na ganin akwai baraka tunda har babban jigon jam’iyyar, Bola Tinubu ya fito ya yi wasu zantuka kan rijistar, Yari ya ce:

“Eh akwai rashin fahimta. Dama ba za ka tara mutum miliyan uku a kan al’amari guda ace sai kowa ya je shafi daya ba. Za a samu rashin fahimta.

“Watakila shi Tinubu bai fahimci abun da ake magana ba shi yasa kila ake ganin cewa akwai bata lokaci cikin wadannan abubuwan. Amma mu a gurinmu muna ganin cewa ba bata lokaci bane.”

Da aka tambaye shi kan ko an zauna a cimma matsaya ba tare da Tinubu bane shiyasa bai fahimci abun ba, Yari ya ci gaba da cewa:

“Toh bani da labari a kan wannan. Amma ni na san cewa mun halarci taro na kokas, kuma na tabbata yana ciki. Kuma an tada wannan tambayan kuma an tattaunata kuma an yanke wannan hukuncin cewa za a yi kuma an zartar, don haka ba zan ce ba ya ciki ba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin Najeriya 36 sun yi ittifakin haramta kiwon shanu a fili

“Amma ko kana cikin magana akwai yanda zai yi wu a yi magana kila kai bai yi daidai da ra’ayinka ba. Kuma idan ka fita ba za a hana ka fadi ra’ayinka ba."

A gefe guda, mun ji cewa aikin yi wa ‘ya ‘yan jam’iyyar APC rajista ya zama abin da ya zama. Jaridar The Nation ta ce rikici sun barke a wasu jihohi a dalilin wannan aiki.

Rahotanni sun tabbatar da cewa daga cikin inda lamarin ya yi kamari akwai jihohin Delta, Osun da Kwara. A jihar Delta, Sanusi Musa, wanda aka ba nauyin wannan aiki ya yi murabus, da ya ke bayani, ua ce ya samu kansa a wani irin yanayi da ya sa ya bar aikin.

Sakataren riko na jam’iyyar APC na kasa, Chidi Okonji, ya zargi shugaban aikin rajista na jihar Delta, Wilson Anyaegbu, da nuna son kai wajen yin rajistan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng