Abubuwa 4 da za su iya tunzura ficewar Femi Fani-Kayode daga PDP zuwa APC

Abubuwa 4 da za su iya tunzura ficewar Femi Fani-Kayode daga PDP zuwa APC

- Ana ta jita-jitar cewa Femi Fani-Kayode zai bar PDP, ya koma jam’iyyar APC

- Akwai yiwuwar rikicin PDP da harin 2023 zai yi tasiri wajen sauya-shekarsa

- Fani-Kayode ya fito ya na sukar wasu da ake ganin jagorori ne a jam’iyyar PDP

A ‘yan kwanakin nan, kusan babu labarin da ake yi kamar na Cif Femi Fani-Kayode wanda ake rade-radin zai sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC.

Kafin yanzu, Femi Fani-Kayode ya yi kaurin-suna wajen sukar jam’iyyar ta APC mai mulki, wanda ya na cikin ‘ya ‘yanta na farko a Najeriya.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin dalilan da ake tunani su ne za su jawo gawurtaccen ‘dan adawar ya koma jam’iyyar da ba ya ga maciji da ita a baya.

Ga wasu daga cikin dalilan da ake tunani:

KU KARANTA: Tinubu ya yi ritaya daga siyasa kawai, APC ta gama da shi - FFK

1. Rikicin cikin gidan PDP

Jam’iyyar hamayya ta PDP ta na fuskantar matsalolin a gida, babu mamakin FFK ya na cikin wadanda ba su jin dadin jagorancin Prince Uche Secondus, don haka yake neman kofa.

2. Zaben 2023

Wani dalili da zai iya jawo Fani-Kayode ya fice daga PDP shi ne harin siyasar 2023. Ana rade-radin PDP za ta sake ‘Dan Arewa ne a 2023, abin da wasu ‘Yan Kudu ba za su so ba.

3. Sabani da manyan gwamnoni

Wata matsala da ke damun jam’iyyar PDP ita ce yadda ake zargin wasu gwamnonin jihohi irinsu Nyesom Wike su ke rike da akalar jam’iyyar, su ke yin duk abin da su ka ga dama.

Abubuwa 4 da za su iya tunzura ficewar Femi Fani-Kayode daga PDP zuwa APC
Manyan APC da Femi Fani-Kayode Hoto: @realFFK
Asali: Twitter

KU KARANTA: Femi Fani Kayode ya yi mani maganar shiga APC - Gwamna

4. Atiku Abubakar

Bayan rashin jituwarsa da kusoshin jam’iyya, da alamu Femi Fani-Kayode ba ya dasa wa da jagoransu, Atiku Abubakar, har kuma ya fito fili ya soki alakarsa da Ahmad Gumi.

A baya an taba jin tsohon ministan harkokin jirgin saman, ya na sukar shirin da uwar jam’iyya ta ke yi na karbe PDP daga hannun gwamna Ben Ayade a Kuros-Riba.

'Dan siyasar ya soki shirin da ya ce wasu na yi a jam’iyyar PDP, ya ce muddin aka yi haka, shi da wasu za su fice su bar PDP domin nuna tsantsar rashin goyon bayansu.

Fani Kayode ya ce idan har ba a dauki matakin gyara ba, shi da wasu 'yan jam’iyya za su iya barin PDP.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai (Info Mgt), kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @mmalumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng