Ni fa ina sake jaddadawa, ba Buhari ke mulkin kasar nan ba: Farfesa Wole Soyinka

Ni fa ina sake jaddadawa, ba Buhari ke mulkin kasar nan ba: Farfesa Wole Soyinka

- Babban farfesan ilimin Turanci, Wole Soyinka, ya bayyana ra'ayinsa game da shugaba Buhari

- Soyinka ya ce magana akan Buhari kan iya zautar da shi

- Ya dawo Najeriya ne a shekarar 2016 bayan da Trump yaci zaben shugaban Amurka

Farfesa Wole Soyinka ya jaddada cewa shi fa bai yarda shugaba Muhammadu Buhari ke mulkin kasar nan ba.

Soyinka ya bayyana hakan yayin jawabi kan matsalar tsaro a wani shirin Arise TV.

Ya ce dubi ga irin abubuwan dake faruwa a fadin tarayya, bai tunanin Buhari ya san abubuwan dake faruwa tsakanin manoma da makiyaya.

"Na dade ina fadin wannan kuma ina sake jaddadawa, Buhari bai san abubuwan dake faruwa ba. Bai fahimci halin da ake ciki ba," Soyinka yace.

"Saboda a fahimta ta, ba zai yiwu shugaban kasa, shugaban jami'an Sojojin kasa ya ce shi ke jagoranci amma abubuwa su tabarbare haka ba, lallai akwai babban matsala cikin lamarin shugabancin kasar nan."

Wole Soyinka ya yi fashin baki kan rahoton cewa makiyaya sun kai hari gidansa dake jihar Ogun.

Ya ce kawai wasu shanu ne suka shiga gidansa kuma ya kore su.

KU KARANTA: Rashin tsaro: A haramtawa makiyayan kasashen ketare shigowa kasar nan, Ganduje

Ni fa ina sake jaddadawa, ba Buhari ke mulkin kasar nan ba: Farfesa Wole Soyinka
Ni fa ina sake jaddadawa, ba Buhari ke mulkin kasar nan ba: Farfesa Wole Soyinka
Source: UGC

KU DUBA: Ina ganin El-Rufa'i bai fahimci matsalar rashin tsaro ba, Ganduje

Mun kawo muku cewa hukumar 'yan sandan jihar Ogun ta sanar da cewa shanun da suka kutsa cikin gidan Wole Soyinka na wani bayerabe ne.

A yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba, Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ya ce shanun na wani Kazeem Sorinola ne wanda ya dauka wani bafulatani wanda yake kula da shanun.

"Shanun na wani bayerabe ne mai suna Kazeem Sorinola. Ya bai wa wani bafulatani kula da shanun ne. Shanun ba na bafulatanin bane, dan tsaro ne kawai," Oyeyemi yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel