Shugaba Buhari ya ba wasu matasa 110 aiki daga kammala shirin bautar kasa saboda kokarinsu
- An zabi wasu zakukurai daga cikin matasan da su ka yi bautar kasa a 2018/19
- Shugaba Muhammadu Buhari ya ba wadannan matasa su 110 aiki a gwamnati
- Gwamnatin kasar ta ba wadanda aka zaba kyautar kudi da damar karo karatu
Fadar shugaban kasa ta ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya raba ayyuka ga wasu matasa 110 da su ka yi wa kasa hidima a kakar shekarar 2018/19.
Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya fitar da jawabi, ya sanar da cewa an ba wadannan matasa aiki kai-tsaye a gwamnatin tarayya.
Bugu da kari, an ba su damar zuwa makaranta su kara karatu har su kai matakin digir-digir (PhD), za su iya yin karatun a duk wata jami’ar gida da suke sha’awa.
Har ila yau, da ya ke magana wajen bikin karrama wadannan tsofaffin ‘yan bautar kasa, shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin za a ba su kyautar kudi.
KU KARANTA: Ma’aikatan Jami’a sun tafi yajin-aiki, sun ba jama'a hakuri
Shugaban kasa ya bukaci hukumomin gwamnati su yi maza su tabbatar da alkawuran da ya yi wa wadannan Bayin Allah, da ya ce sun bauta wa Najeriya da kyau.
An yi la’akari da kokarin da wadannan matasa su ka yi a shirin horo, aikinsu na PPA da CDS na taimakon al’umma da shirin bankwana da ake yi a tsarin na NYSC.
Shugaba Buhari ya taya wadanda su ka yi dacen murna a madadin al’umma da gwamnatin Najeriya, ya kuma ce ya na alfahari da irin irin hidimar da su ka yi.
Mai girma Muhammadu Buhari ya yi amfani da wannan dama, ya yabi sahun farko na matasan da su ka fara yi wa Najeriya hidima ta NYSC shekaru 48 da su ka wuce.
KU KARANTA: Tsagerun Neja-Delta sun sha ban-bam da 'yan bindiga
Haka zalika, Buhari ya yi magana da Janar Yakubu Gowon, wanda ya kirkiro wannan shiri da yake mulki.
A yau ne ku ka ji cewa John Nwodo ya jagoranci wata tawaga da ta tafi har majalisar tarayya, su na fafutukar ganin an kirkiro wata sabuwar jiha a kasar Inyamurai.
Nwodo da sauran manyan Ibo su na neman a ba su sabuwar Jiha da za a barka daga bangaren Enugu, su ka ce an amince da wanan roko tun a taron kasa na 2014.
Shugabannin Majalisar Tarayya sun ce za su goyi bayan a bada wannan sabuwar Jiha ta Adada.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai (Info Mgt), kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. A bibiye shi a Twitter @mmalumfashi
Asali: Legit.ng