Giadom: Ka yi ritaya daga harkar siyasa kawai – FFK ga Bola Tinubu

Giadom: Ka yi ritaya daga harkar siyasa kawai – FFK ga Bola Tinubu

A yayin da ake kokarin kashe wutar rikicin cikin gidan jam’iyyar APC, fitaccen ‘dan adawar nan, Femi Fani-Kayode, ya tsoma bakinsa a lamarin, inda har ya bayyana yadda za ta kaya.

Femi Fani-Kayode ya ba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu shawarar abin yi a rigimar APC. Tsohon ministan ya bayyana haka ne a shafukansa na Facebook da Twitter a jiya ranar Laraba.

Mista Femi Fani-Kayode ya yi kira ga babban jagoran APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi ritaya daga siyasa, ya kuma janye goyon bayansa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Fani-Kayode ya yi wanan magana ne bayan shugaban kasar ya yi wa Victor Giadom a matsayin mukaddashin shugaban APC a daidai lokacin da kotu ta dakatar da Adams Oshiomhole.

Ga abin da Fani-Kayode ya rubuta:

“Da farko aka yi fatali da (Adams) Oshiomhole ta kotun daukaka kara. Sai kuma wanda aka so ya maye gurbinsa a jam’iyya, Abiola Ajimobi ya fada gargara.”

KU KARANTA: Ba na goyon bayan kowa a rigimar da ta kunno kai a APC - Amaechi

Giadom: Ka yi ritaya daga harkar siyasa kawai – FFK ga Bola Tinubu
Femi Fani - Kayode Hoto: Daily Post
Asali: Depositphotos

Femi Fani-Kayode ya kara da cewa:

Sai kuma aka zakulo babban ‘dan adawarsa (Victor) Giadom, wanda Buhari ya yarda da shi a matsayin shugaban jam’iyya na kasa na rikon kwarya.”

“Abin nufi: Ta karewa Asiwaju Bola Ahmed (Tinubu). An yi jifa da shi daga cikin motar jam’iyyar APC, kuma an yi masa ritaya daga siyasa.”

Ana tunanin cewa tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu ya na cikin manyan wadanda su ka tsayawa Adams Oshiomhole, kuma ‘dan siyasar ya na harin kujerar shugaban kasa a 2023.

Masu hasashen siyasa su na ganin cewa wadanda ke adawa da Bola Tinubu ne su ke kokarin yin waje da Adams Oshiomhole daga jam’iyyar APC, wanda hakan na iya kawo masa cikas.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel