Zama da ‘Yan bindiga ne hanyar kawo zaman lafiya – Matawalle ya fadawa Gwamnoni

Zama da ‘Yan bindiga ne hanyar kawo zaman lafiya – Matawalle ya fadawa Gwamnoni

- Gwamnan Zamfara ya bada shawarar yadda za a dumfari matsalar rashin tsaro

- Bello Matawalle ya ce zama ayi sulhu ne hanyar da ta fi kyau ayi amfani da ita

- Gwamnan ya ce idan wasu sun ki bari a zaunan, sai jami’an tsaro su hallaka su

Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara ya bayyana cewa sulhu ne hanya mafi sauki da za a bi wajen shawo kan matsalar ‘yan bindiga a kasar nan.

The Cable ta rahoto gwamnan ya na wannan bayani a lokacin da ya ke amsa tambaya daga bakin ‘yan jarida a lokacin da ya kai ziyara zuwa Yola, jihar Adamawa.

Gwamnan ya yi kira ga sauran takwarorinsa a jihohi su yi amfani da hanyar lalama da miyagun ‘yan bindiga domin ayi maganin matsalar rashin tsaron.

Akasin ra'ayin Nasir El-Rufai, gwamna ya ce sulhu ce hanya mafi kyau kuma tilo da za a bi domin rikicin ‘yan bindiga ya zama tarihi a Zamfara da sauran jihohi.

KKU KARANTA: Ba na goyon bayan ayi wani sulhu da ‘Yan bindiga – El-Rufai

“Ya rage wa jami’an gwamnati ta rungumi zaman sulhu, a tattauna” inji Bello Matawalle.

“Na saba fada cewa hanyar da ta fi, kuma abin da ya rage mana mu yi maganin matsalar shi ne mu nemi a zauna da ‘yan bindiga domin' ayi sulhu.”

“Idan har mu na so mu ga karshen wannan ta’adi, dole mu zauna a tebur, mu sasanta, domin ta hanyar sulhu da lalama, mun iya ceto mutane da yawa da aka sace.”

“Wadanda su ka ki zama ayi sulhu, sai mu yake su, domin a matsayina na gwamna, babban abin da ke gaba na shi ne in samar da zaman lafiya.” Inji gwamnan.

KU KARANTA: Bai dace Gumi ya hada ‘Yan bindiga da tsageru Neja-Delta ba - PANDEF

Zama da ‘Yan bindiga ne hanyar kawo zaman lafiya – Matawalle ya fadawa Gwamnoni
Gwamna Bello Matawalle Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Gwamnan ya ce idan wasu sun ki bari ayi sulhu, sai jami’an tsaro su buda masu wuta. Wannan ya sha ban-bam da ra'ayin masu ganin cewa babu dalilin sulhu da miyagu.

Kamar yadda hukumar dillacin labarai ta bayyana, gwamnan ya kai ziyara zuwa jihar Adamawa ne domin shaida gina wasu hanyoyi da aka yi a karkara.

Bayan haka, an raba kayan aiki, an gudanar da taron ne a garin Kuya-Gaya, karamar hukumar Hong.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel