El-Zakzaky da matarsa basu halarci shari’arsu da gwamnatin Kaduna ba

El-Zakzaky da matarsa basu halarci shari’arsu da gwamnatin Kaduna ba

- Sharia tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da El-Zakzaky, an bayyana Zakzaky bai halarci zaman ba na wannan makon

- Gwamnatin jihar Kaduna ta shiga shari'a da El-Zakzaky da tuhumarsa da laifi sama da takwas

- A baya an bayyana cewa, matar El-Zakzaky ta kamu da Korona, kafin daga baya gidan yari suka karyata

Shugaban Harkar Musulunci a Nijeriya (IMN), Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matar sa, Zeenat ba su halarci kotu ba yayin ci gaba da shari’ar su a ranar Litinin a Babbar Kotun Jihar Kaduna.

Daily Trust ta ruwaito cewa an tsaurara matakan tsaro a babban birnin jihar tare da toshe duk hanyoyin da ke zuwa harabar Kotun Koli wanda ya haifar da babbar matsalar zirga-zirga.

Lauyan mai shigar da kara, Dari Bayero ana sa ran zai kawo sauran shaidun da suka hada da GOC na sojojin Najeriya a zaman kotun.

KU KARANTA: Ahmed Musa zai koma kungiyar kwallon kafa ta West Brom

El-Zakzaky da matarsa basu halarci shari’arsu da gwamnatin Kaduna ba
El-Zakzaky da matarsa basu halarci shari’arsu da gwamnatin Kaduna ba Hoto: Vanguard News
Asali: UGC

Lauyan masu gabatar da kara ya fara gabatar da shaidu biyu daga Sojojin Najeriya wadanda suka bayar da shaida a asirce a gaban kotun.

Wani Darakta daga hukumar tsaro ta jihar da kuma wasu mazauna Gyallesu su uku a Zariya suna daga cikin shaidu hudu da aka karba a matsayin shaidu.

El-Zakzaky da matarsa ​​suna fuskantar shari'a kan tuhume-tuhume takwas da suka hada da zargin kisan kai, yin taro ba bisa ka'ida ba da kuma kawo cikas ga zaman lafiyar jama'a.

Akwai kuma suran tuhume-tuhumen, inda dukkansu suka ki amsa laifin a ranar 29 ga Satumba, 2020.

Su duka biyun suna tsare a gidan Yari da ke Kaduna tun dawowarsu daga jinya zuwa Indiya bisa umarnin kotu.

Daily Trust ta ruwaito cewa mambobin IMN din sun fito kan tituna don sabunta kiranye-kirayen a sake su, suna masu cewa Zeenat El-zakzaky ta kamu da COVID-19 a cikin gidan da ake tsare da ita.

KU KARANTA: PDP ta zargi gwamnatin tarayya da sake kan Korona na biyu

A wani labarin, Hukumar gidan gyara hali ta Najeriya ta yi watsi labaran da ke yawo cewa matar shugaban kungiyar yan uwa Musulmai na shi’a, Zeenat Ibrahim El-Zakzaky ta kamu da korona a inda ake tsare da ita a Kaduna.

A wata sanarwa daga mai magana da yawun hukumar ta jihar Kaduna, Daniel Wadai, ya ce babu wani daga cikin gidajen jihar da aka samu bullar annobar a ciki, saboda suna tabbatar da an bi ka'idojin da aka shimfida na dokar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel