Ban bar harkar fim don na fi karfinta ba, Fati Muhammad ta bayyana dalilinta na barin Kannywood

Ban bar harkar fim don na fi karfinta ba, Fati Muhammad ta bayyana dalilinta na barin Kannywood

- Shaharrariyar tauraruwar fina-finan Kannywood Fati Muhammad ta amsa wasu tambayoyi kan abubuwan da suka shafi rayuwarta

- A tattaunawar da aka yi da ita, Fati ta bayyana cewa ta bar masana'antar shirya fina-finan Hausa ba don ta fi karfinta ba, illa don shekaru da lokacinta da suka ja baya

- Ta kuma bayyana cewa ra’ayi da kaddara ne suka sa ta tsunduma harkar siyasa a yanzu

Shahararriyar tsohuwar jarumar nan ta Kannywood, Fati Muhammad ta bayyana abunda ya sa ta barin harkar fim.

A cewar jarumar, ta bar fim ne ba wai don ta fi karfin yin sa ba, illa kawai ta ce idan lokacin mutum da shekarunsa suka ja ya kamata ya bar na baya su shigo a dama da su.

A wata hira da tayi da sashin Hausa na BBC Fati ta bayyana cewa a zamanin da take harkar fim, ta fi so a hada ta da shahararren jarumi Ali Nuhu, wanda a cewarta ko yan kallo suna ganin sun fi dacewa da junansu.

Ban bar harkar fim don na fi karfinta ba, Fati Muhammad ta bayyana dalilinta na barin Kannywood
Ban bar harkar fim don na fi karfinta ba, Fati Muhammad ta bayyana dalilinta na barin Kannywood Hoto: fatymuhd
Source: Instagram

Ta kuma bayyana cewa Abida Muhammed ce babbar kawarta wacce a tare suka yi zamani da kuma tashe a masana’antar shirya fina-finan.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojojin Najeriya ta karyata cewar 'yan ta'adda sun kashe sojoji 20 a arewa maso gabas

Har ila yau, da aka tambaye ta game da wata boyayyiyar baiwa da take da ita, jarumar ta ce a matsayinta na Bafulatana, tana iya kallon saniya ta tsatsi madara daga cikinta sannan ta dafa shi ya zama kindirmo wanda ba kowa ne ya san ta iya hakan ba.

Kan dalilinta na shiga harkar siyasa, Fati ta ce ra’ayi da kaddara ne suka kaita ga shiga lamarin siyasa tare da son mutumin da take goya wa baya wato Alhaji Atiku Abubakar.

Ta kuma bayyana cewa abunda ba za ta taba mantawa da shi ba, shine labarin mutuwarta da aka ta yadawa a lokain da take ganiyar tashe a masana’antar Kannywood, inda tace abun ya taba mata zuciya sosai kasancewar ita ce jaruma ta farko da aka fara yada wannan labarin karyar a kanta.

KU KARANTA KUMA: Jihohin Najeriya 11 da basu jawo hankalin masu saka hannun jari na kasashen waje ba a cikin shekaru 2

Daga karshe ta roki Allah ya bata miji na gari domin ta rufa wa kanta asiri sannan ta samu zuri’a dayyiba, a cewarta wannan shine babban burinta a yanzu.

A wani labarin, ‘Yar wasar fim, Grace Ifemeludike, ta ba mazan da su ke yaudarar matan aurensu shawarar su rungumi auren mata da yawa domin su daina lalata da mata.

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Daily Nigerian, Grace Ifemeludike wanda jarumar Nollywood ce, ta yi wannan kira ne a shafinta na Instagram.

Da ta ke magana a ranar Talata, 9 ga watan Fubrairu, 2021, Grace Ifemeludike, ta yi Allah-wadai da yadda zina ta zama ruwan dare tsakanin mazaje a Afrika.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel