Majalisa ta ba Buhari, Jami’an tsaro satar-amsa 6 domin shawo kan matsalar tsaro

Majalisa ta ba Buhari, Jami’an tsaro satar-amsa 6 domin shawo kan matsalar tsaro

- Sanatoci sun ce akwai bukatar a duba halin rashin tsaro da ake fama da shi

- ‘Yan Majalisar sun bada shawara ayi wa tsarin tsaro na kasar garambawul

- An yi kira ga Jami’an tsaro su tura jirage su tsefe dajin da ‘yan bindiga suke

A ranar Laraba, 10 ga watan Fubrairu, 2021, majalisar dattawa ta fada wa jami’an tsaro suyi amfani da jiragen yaki domin bankado ‘yan bindigan da ke jeji.

Jaridar Punch ta ce shugaban majalisar dattawan kasar, Ahmad Ibrahim Lawan ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayanin matsayar da majalisa ta dauka.

Sanatoci irinsu Tolulope Odebiyi, Solomon Adeola, Ademola Balogun, da Ali Ndume su ka ce akwai bukatar ayi wani abin game da sha’anin tsaro a kasar.

Matsayar ‘yan majalisar dattawar ita ce ayi kira ga shugaban kasa ya bada umarni ga NSA da sababbin hafsun sojoji da IGP ayi wa harkar tsaro garambawul.

KU KARANTA: Sojoji sun dakile harin Boko Haram

Sanatocin sun bada shawarar a aika jiragen sama marasa direba da jirage masu saukar ungulu zuwa kungurman dajoji da nufin murkushe miyagun ‘yan bindiga.

An kuma bukaci gwamnatin tarayya ta duba yadda makamai su ke barko wa, tare da kawo dokar da za ta sa a cafke wadanda ke rike da bindigogi ba tare da izini ba.

Bayan haka, sanatocin sun yi kira ga gwamnonin jihohi su dabbaka shirin National Livestock Transformation domin ayi maganin rikicin makiyaya da manoma.

Har ila yau, sanatocin kasar sun bada shawara a bada kayan aiki ga jami’an kwastam da masu kula da shige da fice domin a tsare kan iyakokin kasar nan da kyau.

KU KARANTA: Buhari ya fada mana mu murkushe 'Yan Boko Haram inji Amao

Majalisa ta ba Buhari, Jami’an tsaro satar-amsa 6 domin shawo kan matsalar tsaro
Shugaban Majalisa, Ahmad Ibrahim Lawan Hoto: @NgrSenate
Source: Twitter

A karshe an bukaci gwamnatin tarayya ta sake bibiyar yarjejeniyar ECOWAS wanda ta halatta zirga-zirga babu kaidi, domin a hana miyagu shigo wa Najeriya.

A ranar Laraba kun ji cewa sababbin hafsoshin tsaron za su bayyana a majalisa inda za su sha tambayoyi domin a tantance su kamar yadda dokar kasa ta bukata.

Majalisar wakilan tarayya ta nada wani kwamiti na musamman da zai soma aiki a kan nade-naden shugabannin tsaro da mai girma Muhammadu Buhari ya yi.

‘Yan Majalisar tarayyar za su yi wa sababbin hafsoshin tsaron da Buhari ya nada tankade da rairaya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel