Fani-Kayode ya yi kus-kus da Jonathan cikin dare ana tsakar rade-radin zai koma APC

Fani-Kayode ya yi kus-kus da Jonathan cikin dare ana tsakar rade-radin zai koma APC

- Femi Fani-Kayode ya hadu da Dr. Goodluck Jonathan a gidansa da ke Abuja

- Tsohon Ministan bai bayyana makasudin zaman na sa na jiya da Jonathan ba

- ‘Dan siyasar ya zauna da tsohon shugaban ne bayan ya hadu da manyan APC

Tsohon Ministan Najeriya, Femi Fani-Kayode ya tabbatar da cewa ya yi wani zama da tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan.

Mista Femi Fani-Kayode ya kai wa tsohon shugaban Najeriyar ziyara ne a gidansa da ke garin Abuja, a a ranar Talata, 9 ga watan Fubrairu, 2021.

Fani-Kayode wanda ake radi-radin zai sauya-sheka ya koma jam’iyyar APC ya kai wa Goodluck Jonathan ziyara har gida ne tare da tawagarsa a jiya.

“Tawagata da ni kai na mun samu alfarma da damar yini tare da (tsohon) shugaba Goodluck Jonathan a gidansa na babban birnin tarayya Abuja."

KU KARANTA: Zaman 'Yan APC da FFK bai dame mu ba - PDP

FFK kamar yadda aka fi saninsa, ya yabi tsohon shugaban Najeriyar, wanda ya ce babu irinsa.

‘Dan siyasar ya tabbatar da cewa an yi wannan zama ne a ranar Talata cikin dare. Ya rubuta a shafinsa na Twitter, @realFFK “Babu wani irinsa!”

A baya, FFK ya yi karin-haske: “Ina ba mutanen Najeriya shawara su yi hattara da kalaman karyar da ake kakaba mani a kan shugabannin siyasar kasar nan.”

“Idan ba ku ji wani abu daga gare ni a ainihin shafukana na Twitter ko Facebook ba, to ban fada ba. Iyakar ta kenan.” Fani-Kayode a shafinsa na Twitter.

KU KARANTA: Kungiyar matasa tana maraba da Fani-Kayode a APC

Fani-Kayode ya yi kus-kus da Jonathan cikin dare ana tsakar rade-radin zai koma APC
Fani-Kayode da mutanensa a gidan Goodluck Jonathan Hoto: @realFFK
Asali: Twitter

Kayode ya rike matsayin hadimin shugaban kasa, kuma ya taba yin Ministan harkokin jiragen sama da na al’adu a gwamnatin PDP ta Olusegun Obasanjo.

Wannan ziyara ta na zuwa ne bayan babban jigon na jam’iyyar PDP a kudancin Najeriya ya gana da wasu kusoshin APC, har da shugaban riko, Mala Buni.

Fani-Kayode ya ce sun yi zaman ne domin tattauna batutuwan da suka shafi Najeriya da siyasa da nufin kare al'umma daga tsinduma wa cikin yakin basasa.

FFK ya ke cewa a matsayinsu na dattawan kasar nan, idan matsala ta taso gadan-gadan, dole ne a ajiye siyasa a gefe a hada kai, domin kawo cigaban al'umma.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel