Ahmad Lawan ya caccaki mai taimaka masa saboda rashin sanya takunkumin fuska

Ahmad Lawan ya caccaki mai taimaka masa saboda rashin sanya takunkumin fuska

- A baya gwanmnatin tarayya ta sanya dokar dole a sanya takunkumin fuska a kebabben wurare

- Ana ci gaba da bin, sai dai akan samu har wasu jami'an gwamnati da ke karya wannar dokar

- A ranar Laraba, shugaban majalisar dattijai ya caccaki wani a farfajiyar majalisa don ya karya dokar

Shugaban majalisar dattijai Ahmed Lawan a ranar Laraba ya caccaki wani mai taimaka wa majalisar kan rashin sanya takunkumin fuska a harabar Majalisar Dokoki ta Kasa, The Nation ta ruwaito.

Wata sanarwa da Mista Ezrel Tabiowo, mataimaki na musamman kan harkokin manema labarai a ranar Laraba a Abuja, ya ce Lawan yana shiga harabar Majalisar Dokoki ta kasa lokacin da ya hango mai taimaka masa, yana tsaye a harabar babu takunkumin fuska.

KU KARANTA: Watanni 5 bayan turawa Rarara kudade, har yanzu batun wakar Buhari shiru

Ahmad Lawan caccaki mai taimaka masa saboda rashin sanya takunkumin fuska
Ahmad Lawan caccaki mai taimaka masa saboda rashin sanya takunkumin fuska Hoto: The Nation
Source: UGC

Ya ce da Shugaban Majalisar Dattawan ya gan shi, sai ya tsayar da shi ya caccakeshi saboda bai sanya takunkumin fuska ba, “ina takunkumin fuskar ka,

"Mai taimaka wa majalisar wanda ba ya tsammanin tambayar, ya yi shiru, yana cikin aljihu na, yallabai, yayin da yake kokarin yin fito na fito da fuskar sa daga aljihunsa," in ji shi.

Lawan ya ci gaba da kallonsa yayin da mataimakin ke kokarin kaiwa ga neman takunkumin fuskarsa, daga nan ya zarce zuwa ofishin sa.

KU KARANTA: Gwamnati ta daskare asusun bankin Sunday Igboho, ya yi martani

A wani labarin, Shugaban majalisar dattijai, Yahaya Abdullahi, ya ce zauren dattijai zai tattauna kan matsalar rikicin makiyaya Fulani a duk fadin kasar a ranar Talata, jaridar Punch ta ruwaito.

Abdullahi, wanda ya zanta da manema labarai a ofishinsa, ya ce mataimakinsa wanda ke wakiltar Ondo ta Arewa a Majalisar Dattawa, Farfesa Ajayi Boroffice, zai gabatar da kudiri kan batun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel