Wata sabuwa: Mabarata a jihar Jigawa sun hana gwamna fita daga cikin gidansa

Wata sabuwa: Mabarata a jihar Jigawa sun hana gwamna fita daga cikin gidansa

- Wasu mabarata a jihar Jigawa sun garkame gidan gwamnan jihar don ya saurare su

- A yayin jaddada rajistarsa, gwamnan ya samu tseko daga mabaratan da suke kokawa kan yunwa

- Marabaratan sun hana 'yan jarida da manyan mutanen garin ganawa da gwamnan

Wasu gungun mabarata da galibinsu mata ne, sun yiwa gidan gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar kawanya. Sun nemi kuɗi, suna cewa suna jin yunwa, The Nation ta ruwaito.

Gwamnan ya je Babura ne, mahaifar kasarsa, don sake jaddada zamansa mamba a jam’iyyar APC a mazabarsa da ke Kofar Arewa Primary School.

Nan da nan ya shiga harabar gidansa bayan da ya sake jaddada rajistar jam'iyyarsa a garinsu, mabaratan suka kewaye gidansa.

An yi zargin cewa wata 'yar karamar hasuma ta faru lokacin da mabaratan suka kewaye gidan gwamnan suna neman a basu kudi, kuma sun bayyana cewa rayuwa na yi musu kunci.

Mabaratan sun taru a gidan gwamnan domin ya saurare su. Amma bai samu fitowa ba.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: WTO za ta nada Darakta-Janar a ranar Litinin mai zuwa

Wata sabuwa: Mabarata a jihar Jigawa sun hana gwamna fita daga cikin gidansa
Wata sabuwa: Mabarata a jihar Jigawa sun hana gwamna fita daga cikin gidansa Hoto: The Elite Times
Asali: UGC

Matsala ta fara ne a lokacin da mabaratan suka dade a waje suna jiransa ba tare da wata alama da ke nuna cewa gwamnan zai saurare su . Madadin haka, sai jami'an tsaro ke kokarin tarwatsa su. Sun fara ihu kuma sun dauki hanyar shiga harabar.

Su dubbunsu, sun ƙi barin wajen, yayin da suka ingiza jami'an tsaron cikin gidan kuma suka kulle duk hanyoyin shiga gidan gwamnan.

KU KARANTA: Sauya sheka: Kungiyar matasa tana maraba da Fani-Kayode zuwa APC

Lamarin ya sanya manyan mutane da yawa rashin samun damar zuwa gidan gwamnan, ciki har da ‘yan jarida, wadanda aka tilasta su ja da baya saboda tsoron kada gungun mutanen su far masu.

Daya daga cikin matan da suka yi garkuwar da gwamnan a gidansa, Malama Halima Hadi ta ce matsalar su ba COVID-19 ba ne, duk da cewa ta ce akwai batun talauci, rashin aikin yi, da fyade da ke addabar su. Ta kuma ce mutane ba sa iya samun cin abinci sau uku a rana.

A wani labarin, Gwamnoni a Arewa a ranar Talata sun bayyana batun kiwo a fili da makiyaya suke yi a matsayin tsohon abu. Ya kamata ya kare, The Nation ta ruwaito.

Wannan shawarar ita ce sakamakon, taron kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya, wanda aka gudanar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel