Shugaba Buhari ya kaddamar da aikin ginin layin dogon Kano-Jigawa-Katsina-Maradi

Shugaba Buhari ya kaddamar da aikin ginin layin dogon Kano-Jigawa-Katsina-Maradi

- Bayan watanni biyar da amincewa da aiki, za'a fara ginin layin dogo daga Najeriya zuwa Nijar

- Gwamnatin tarayya na kyautata zaton cewa wannan layin dogo zai inganta kasuwanci

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya kaddamar da aikin ginin layin dogon da zai ratsa Kano-Dutse-Jibiya har zuwa Maradi a jamhurriyar Nija mai tsayin kilomita 284.

Buhari ya kaddama da aikin ginin ne ta yanar gizo a fadar shugaban kasa, Aso Villa, dake birnin tarayya Abuja.

A watan Satumba 2020 ne majalisar zartaswar tarayya ta amince da kashe dala bilyan 1.96 wajen gina layin dogon.

A cewar shugaba Buhari yayin kaddamar da aikin ginin, ya ce kamfanin Mota-Engil Group ne zai yi aikin kuma zai gina jami'a na musamman don ilmantar da yan Najeriya kan fasahar layin dogo.

"Kamfanin da zai yi wannan aikin, Messrs Mota-Engil Nigeria Limited, zai bada gudunmuwa wajen bada ilmi da fasaha ta hanyar gina jami'an sufuri da fasahar layin dogo. Wannan abin yabo ne," Buhari yace.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta kashe N37bn a tallafin 'Survival Fund', in ji Osinbajo

An sa ran kammala aikin cikin shekaru uku masu zuwa kuma ana kyautata zaton zai inganta harkokin kasuwanci a Kano, Katsina Jigawa da kuma Maradi a Nijar.

Daga cikin wadanda suka halarci taron kaddamarwan akwai gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari; gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru; gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje; da gwamnan jihar Maradi a Nijar, Zakaru Umar.

Sauran kuwa akwai Ministoci, wanda ya hada da ministan labarai, Alhaji Lai Mohammed, sa sarakunana gargajiya daga Najeriya da jamhurriyar Nijar. (NAN)

Shugaba Buhari ya kaddamar da aikin ginin layin dogon Kano-Jigawa-Katsina-Maradi
Shugaba Buhari ya kaddamar da aikin ginin layin dogon Kano-Jigawa-Katsina-Maradi Credit: @BuhariSallau1
Asali: Twitter

DUBA NAN: Kungiyoyin Arewa suna marawa Gumi baya kan samar da filayen kiwo ta kasa

A bangare guda, ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya fada a ranar Litinin cewa cin hanci da rashawa ya ci gaba a kasar ne saboda wadanda suka bayyana barayi ba a daure su ko kuma hukunta su, jaridar.

Amaechi, wanda ya yi magana a lokacin da yake gabatar da lacca ta 2021 na Jami’ar Fatakwal, ya bukaci jama’a su daina yin bikin girmama mutanen da suka wadata kansu ta hanyar satar dukiyar jama’a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng