Ayarin motocin Zulum sun yi hatsari, mutum 2 sun rasa rayukansu

Ayarin motocin Zulum sun yi hatsari, mutum 2 sun rasa rayukansu

- Hatsarin mota ya cika da ayarin motocin Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno

- Lamarin wanda ya afku a ranar Talata, 9 ga watan Fabrairu, ya yi sanadiyar mutuwar wasu mutum biyu

- An kwashi mutane biyu da suka jikkata zuwa asibiti

Mutane biyu sun mutu sakamakon hatsarin da ya cika da ayarin motocin gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum.

Jaridar TheCable ta fahimci cewa lamarin ya faru ne a safiyar ranar Talata, 9 ga watan Fabrairu yayin da gwamnan ke kan hanyarsa ta zuwa Maiduguri.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: 'Yan bindiga sun sace hadimin mataimakin gwamnan Taraba

Ayarin motocin Zulum sun yi hasari, mutum 2 sun rasa rayukansu
Ayarin motocin Zulum sun yi hasari, mutum 2 sun rasa rayukansu Hoto: @IamMkyari/Twitter, Engr. Dr. Babagana Umara Zulum/Facebook
Asali: UGC

Zulum na dawowa ne daga karamar hukumar Mafa (LGA) inda ya je sabonta rijistarsa na dan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) lokacin da hatsarin ya faru

Wata majiyar ‘yan sanda da ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce wani basarake na daga cikin wadanda suka mutu

A cewar 'yan sandan, motar da ke dauke da Mai-Kanuribe, wani hakimin Borno da ke Legas, ta kife bayan da tayar ta fashe, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa da kuma wani fasinja guda daya.

An garzaya da mutane biyu da suka jikkata zuwa asibiti yayin da aka kai gawarwakin mutanen biyu da suka mutu zuwa Maiduguri.

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: 'Yan daba sun sake tarwatsa wani taron APC a Kwara, sun lalata motoci

Wannan lamarin ya zo ne watanni hudu bayan maharan Boko Haram sun kai wa ayarin motocin Zulum hari sau biyu a cikin mako guda.

A wani labari na daban, Fulani makiyayan dake kudu maso yamma, kudu maso gabas da wasu sassan Najeriya sun bayyana niyar komawa jihar Kano inda aka shirya musu shirin RUGA.

Sakataren kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), a jihar Kano, Zubairu Ibrahim, ya bayyana hakan.

A cewar Ibrahim, makiyayan sun hada wadanda ke zaune a jihar Nasarawa, Neja, Enugu, Oyo, da sauran su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel