Fulani Makiyayan dake kudancin Najeriya sun fara komawa jihar Kano, Miyetti Allah

Fulani Makiyayan dake kudancin Najeriya sun fara komawa jihar Kano, Miyetti Allah

- Sakamakon korar Fulanin da ake yi a wasu jihohin kudu, rahoto ya nuna cewa sun fara komawa Arewa

- Kungiyar dattawan Arewa a makonnin baya ta shawarci makiyaya su koma gida idan ana kinsu

- Amma gwamnati ta bayyana cewa wannan ba shi bane mafita

Fulani makiyayan dake kudu maso yamma, kudu maso gabas da wasu sassan Najeriya sun bayyana niyar komawa jihar Kano inda aka shirya musu shirin RUGA.

Sakataren kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), a jihar Kano, Zubairu Ibrahim, ya bayyana hakan.

A cewar Ibrahim, makiyayan sun hada wadanda ke zaune a jihar Nasarawa, Neja, Enugu, Oyo, da sauran su.

Ya ce tuni makiyaya da wadannan jihohi uku sun koma jihar Kano.

"Mun karbi bakuncin Fulani Makiyaya daga Kebbi, Zamfara, Kaduna, Sokoto da Jigawa, da suka dawo Kano yanzu," Vanguard ta ruwaito Ibrahim da fadi.

DUBA NAN: Za mu dauko Sojin haya daga Chadi da Kamaru don kawar da yan Boko Haram, COAS

Fulani Makiyayan dake kudancin Najeriya sun fara komawa jihar Kano, Miyetti Allah
Fulani Makiyayan dake kudancin Najeriya sun fara komawa jihar Kano, Miyetti Allah
Source: Twitter

KU DUBA: Sheikh AbdulJabbar: Jama'atu Nasril Islam ta jinjinawa Ganduje da Malaman jihar Kano

Kungiyar dattawan Arewa (NEF) a makon jiya ta bayyanawa al'ummar Fulani dake kudancin Najeriya su dawo gida idan ana koransu daga inda suka zaune.

Hakazalika Kungiyar NEF ta yi kiraga gwamnonin Arewa su shirya karban Fulanin dake shirin dawowa gida daga kudu.

Amma Kungiyar kare hakkin Yarbawa a Najeriya, Afenifere, ta caccaki dattawan Arewa kan kiran da sukayi ga Fulani Makiyaya su koma Arewa idan aka cigaba da tsangwamarsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel