Rikicin APC a Kwara: An kwantar da jiga-jigan jam’iyyar 5 bayan musayar naushi da jefe-jefen kujeru da suka yi

Rikicin APC a Kwara: An kwantar da jiga-jigan jam’iyyar 5 bayan musayar naushi da jefe-jefen kujeru da suka yi

- Wani bidiyo ya yi fice a makon nan, inda aka nuno mambobin APC a jihar Kwara suna ba hammata iska da jefa wa junansu kujeru

- An kwantar da wasu jiga-jigan jam’iyyar da suka ji rauni inda suke samun kulawa a wani asibiti da ba a bayyana ba

- Shugaban jam’iyyar, Bashir Bolarinwa, wanda ya ziyarce su ya nuna farin ciki na ganin cewa suna samun lafiya

An ba jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) biyar wadanda suka ji munanan raunuka a rikicin da ya barke a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar reshen jihar Kwara gado a asibiti.

Suna samun kulawar likitoci a wasu asibitoci da ba a bayyana ba a Ilorin, babbar birnin jihar Kwara, jaridar This Day ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Fasto Adeboye ya yi hasashen lokacin da ta’addanci zai zo karshe a Nigeria

Rikicin APC a Kwara: An kwantar da jiga-jigan jam’iyyar 5 bayan musayar naushi da jefe-jefen kujeru da suka yi
Rikicin APC a Kwara: An kwantar da jiga-jigan jam’iyyar 5 bayan musayar naushi da jefe-jefen kujeru da suka yi Hoto: @nannews_ng
Asali: Twitter

Daga cikin wadanda aka kwantar sune:

Alhaji Dantala Yaro, ma’ajin jihar

Wahab Adeshina, mamba a kwamitin hukumar jiragen ruwa ta Najeriya (NPA)

MallamLai Karatu, Shugaban matasa

Alhaja Sidi Gidado, mahaifiyar shugabar mata ta jihar

Salihu Elepo, sakataren karamar hukumar Ilorin ta gabas

Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar a jiharm Hon. Bashir Bolarinwa ya kai wa mutanen ziyarar jaje.

Bolarinwa ya bayyana cewa:

“Ina fari ciki da ganin cewa dukkansu sunyi kwari kuma suna samun dauki.”

A baya mun ji cewa, Bashir Bolarinwa, shugaban riko na jam’iyyar APC a Kwara ya bada labarin yadda aka auka masu da hari a wajen zaman jam’iyya da aka kira a Ilorin.

KU KARANTA KUMA: Dandalin Kannywood: Allah ya yi wa mahaifin shahararren mawaki Ali Jita rasuwa

Bashir Bolarinwa ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan an kira su zuwa wajen rajistar da kwamitin Sanata John Danboyi ya ke yi a dakin taro na Banquet Hall.

A cewar Bolarinwa, har zuwa karfe 1:30 na rana, ba a bude wurin da aka ce za ayi taro da karfe 12:00 ba. Wannan ya sa a aikawa Sanata Danboyi sako ta wayar salula.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel