Mun gano arzikin man fetur mai yawan gaske a wata jihar Arewacin Najeriya, Shugaban NNPC Mele Kyari

Mun gano arzikin man fetur mai yawan gaske a wata jihar Arewacin Najeriya, Shugaban NNPC Mele Kyari

- Da yiwuwan Arewacin Najeriya ta wadatu da arzikin man fetur kamar kudu

- Bayan watanni ana bincike, an gano arzikin mai a tafkin jihar Benue

- Najeriya na haran ajiyar danyen mai akalla gangan milyan 40 domin sayarwa kasashen waje

An gano arzikin man fetur mai dimbin yawa a jihar Benue, kuma masana ilimin ma'adinan Najeriya ke jagorantan hakan, shugaban kamfanin man feturin Najeriya NNPC, Mele Jyari ya bayyana haka.

Kyari ya bayyana hakan ne yayin jawabi a taron bude bikin baja kolin kungiyar masu nema arzikin man fetur na Najeriya (NAPE) a ranar Alhamis.

Ya jaddada cewa kamfanin NNPC ta zage dantse wajen fadada ma'ajiyar arzikin danyen man feturin Najeriya zuwa ganga milyan 40 ta hanyar binciken arzikin a sassan Najeriya gaba daya.

Mele Kyari, wanda ya samu wakilcin shugaban sashen hulda da jama'a na NNPC, Dr Kennie Obateru, ya ce suna daukan wannan mataki na neman arzikin mai ne domin cimma manufar gwamnatin tarayya na cimma gangar danyen mai milyan 4.

"Ina farin cikin yabawa ayyukan kwarai da kuke yi da jajircewarku masananmu wajen neman arzikin mai aka gani a jihar Benue. NNPC na alfahari da mambobin kungiyar NAPE dake jagorantan wannan kokari," Malam Kyari ya bayyana.

KU DUBA: Farfesan Likitancin dabbobi na farko a Arewacin Najeriya, Marafan Nupe, ya rasu

Mun gano arzikin man fetur mai yawan gaske a wata jihar Arewacin Najeriya, Shugaban NNPC Mele Kyari
Mun gano arzikin man fetur mai yawan gaske a wata jihar Arewacin Najeriya, Shugaban NNPC Mele Kyari
Asali: UGC

KU KARANTA: Dangote, Isyaka Rabiu, da wasu attajirai biyu ne biloniyoyin Najeriya 4 a 2020, Forbes

A wani labarin daban, yan Najeriya su shirya hauhawar farashin man fetur kwanan nan a fadin tarayya saboda sabon farashin jigilar mai a Depot da kamfanin PPMC ta kara daga N147.67 zuwa N155.17, Premium Times ta ruwaito.

Kamfanin PPMC, wani sashe ne na kamfanin man feturin Najeriya NNPC, masu shigo da kusan dukkan man feturin da ake amfani a kasar nan.

Farashin man yanzu na iya tashi zuwa N170 da lita a gidajen mai.

A takardar da kamfanin ta saki ranar 11 ga Nuwamba, an gano cewa za'a fara sayar da mai a wannan farashin ranar 13 ga Nuwamba, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel