Sai Jam’iyyarmu ta APC ta shafe tsawon shekara 100 ta na mulki inji Yusuf Gagdi

Sai Jam’iyyarmu ta APC ta shafe tsawon shekara 100 ta na mulki inji Yusuf Gagdi

- Yusuf Gagdi ya yi kuri, ya ce za su yi shekaru 100 su na mulki a Najeriya

- Hon. Gagdi shi ne ‘dan majalisa mai wakiltar Pankshin, Kanke da Kanam

- ‘Dan Majalisar ya ce za a cigaba da zaben APC saboda kokarin da su kayi

Yusuf Gagdi, mai wakiltar mazabar Pankshin/Kanke/Kanam a majalisar wakilan tarayya ya ce APC za ta cigaba da mulki na tsawon shekaru 100.

Honarabul Yusuf Gagdi ya bayyana haka ne bayan ya sabunta rajistarsa na jam’iyyar APC a kauyen Gum-Gagdi, karamar hukumar Kanam, jihar Filato.

Jaridar The Cable ta rahoto ‘dan siyasar ya na cewa jam’iyyar APC mai mulki ta na cigaba da kara farin-jini tun da ta kafa gwamnati bayan zaben 2015.

A cewarsa, jam’iyyar APC ta yi kokari a gwamnati, kuma jama’a za su kada wa jam’iyyar kuri’a a zabe mai zuwa na 2023, da duk wasu zabuka da za ayi.

KU KARANTA: Zaben 2023: Kabiru Gaya ya fara magana a kan takarar Gwamna

“Daga dandazon da na gani a yau, ta tabbata cewa jam’iyyarmu ta APC ta na da mutane a kasa.” Inji ‘dan majalisar yayin da yake jawabi a ranar Asabar.

Ko da cewa Ubangiji ke zaben abin da zai faru, amma ganin nasarorin da mu ka samu a matakai dabam-dabam, za mu cigaba da rike mulki bayan 2023.”

Wannan ‘dan siyasa har ya kai ga cika-baki, ya ce: “Kai ba ma zabe mai zuwa ba kurum, jam’iyyar nan za ta cigaba da rike gwamnati na shekaru 100 masu zuwa.”

Yusuf Gagdi ya ce rajistar da ake yi wa ‘ya ‘yan APC zai ba jam’iyyar damar rike kujerun mukamai domin za a samu karin mabiya da za su shiga tafiyar ta su.

‘Dan Majalisar Filato ya ce Jam’iyyar APC za tayi shekaru 100 a kan mulki
Hon. Yusuf Gagdi Hoto: www.viewpointnigeria.org
Asali: UGC

KU KARANTA: Dalilan da suka sa Tinubu da Akande su ke sukar sabunta rijistar APC

A 2015 APC ta karbe mulki daga hannun PDP, ta kafa gwamnati a Filato, sannan ta samu mulkin kasa.

A karshen makon nan kun ji jam'iyyar APGA ta ba PDP da sauran jam'iyyu mamaki a zaben maye gurbin kujerar majalisar tarayya da aka gudanar a Jihar Neja.

INEC ta gudanar da zabe domin cike gurbin kujerar 'dan majalisa mai wakiltar yankin Magama/Rijau.

Ɗan takarar APGA, Salihu Salleh ya samu kuri'u 22,965 ya lallasa abokin hamayyarsa, Emmanuel Alamu Endoza na jam'iyyar PDP wanda ya samu kuri'u 22,507.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel