2023: Sahihan dalilan da suka sa Tinubu da Akande ke sukar sabunta rijista da APC ke yi

2023: Sahihan dalilan da suka sa Tinubu da Akande ke sukar sabunta rijista da APC ke yi

- Jiga-jigan jam'iyyar APC, Bola Tinubu da Bisi Akande suna sukar sabunta rijistar da ake yi a fadin jam'iyyar APC

- Majiyoyi sun tabbatar da cewa jiga-jigan jam'iyyar na zargin wani kulli na kwace jam'iyyar daga hannunsu baki daya

- Kwamitin rikon kwarya na APC karkashin shugabancin Mai Mala Buni ne ya kaddamar da sabunta rijistar 'yan jam'iyyar a kasar nan

Sabbin dalilai sun bayyana a kan abinda yasa jigon jam'iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu da kuma uban jam'iyya, Bisi Akande da wasu suke sukar sabunta rijistar da 'yan jam'iyyar ke yi a kasar nan.

Fiye da dalilan da shugabannin biyu suka sanar, majiyoyi da suke tattare da su sun ce zargin wani mugun abu zai bullo daga shugabannin jam'iyyar na yanzu sune sahihan dalilan da suka sa Akande da Tinubu suke sukar rijistar.

Kwamitin rikon kwarya da tsari na jam'iyyar karkashin shugabancin Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya fara rijistar 'yan jam'iyyar a fadin kasar nan.

KU KARANTA: Miloniyoyin Najeriya 5 masu karancin shekaru a 2021 da yadda suka tara dukiyarsu

2023: Sahihan dalilan da suka sa Tinubu da Akande basu goyon bayan rijista da APC ke yi
2023: Sahihan dalilan da suka sa Tinubu da Akande basu goyon bayan rijista da APC ke yi. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

An kafa kwamitin a watan Yunin shekarar da ta gabata bayan da aka sallami Adams Oshiomhole, makusancin Tinubu, daga shugabancin jam'iyyar sakamakon rikicin da ya barke a kwamitin gudanarwa na jam'iyyar.

Majiyoyi da dama sun sanar da Daily Trust cewa Tinubu da wasu jiga-jigan jam'iyyar suna zargin rijistar wata kulli ce ta kwace jam'iyyar daga hannunsu.

KU KARANTA: Hotunan kafin aure na matashin da zai yi wuff da kyawawan 'yan mata 2 a rana daya a Abuja

A wani labari na daban, shugaban majalisar sarakunan jihar Zamfara kuma Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmed ya ja kunne a kan auren mace fiye da daya wanda yayi ikirarin shine dalilin tabarbarewar ilimi a kasar nan.

A yayin magana a taron sarakunan jihar 17 da shugaban UBE na jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Aliyu Maradun a Gusau, Sarkin Anka wanda ya fara alakanta talauci da tara mata, yayi kira ga al'ummar Musulmi da su tabbatar da sun bai wa 'ya'yansu ilimi na boko da zamani mai nagarta.

Basaraken ya jaddada goyon bayan sarakunan gargajiya ga ilimin zamani a jihar Zamfara da jama'arta baki daya, Linda Ikeji ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel