Sanata Gaya, yace jama’a sun yaba da ayyukansa, ana rokonsa ya nemi Gwamna a 2023
- Sanata Kabiru Gaya ya ce al’umma sun yaba da aikinsa, su na so ya fito Gwamna
- Gaya ya shafe shekaru ya na wakiltar mazabar Kano ta Kudu a majalisar dattawa
- ‘Dan Majalisar ya ce sai ya zauna da wasu kafin ya yanke shawarar takara a 2023
Sanata Kabiru Gaya (APC Kano), ya ce har yanzu bai yanke shawarar kiran da ake yi masa na ya fito takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2023 ba.
Kabiru Gaya wanda ya taba yin gwamna a jihar Kano ya yi hira da ‘yan jarida a ranar Lahadi, inda ya tabbatar da cewa wasu su na rokonsa ya fito takara.
Jaridar Daily Trust ta ce Kabiru Gaya wanda ya shafe shekara 13 a majalisar tarayya, ya ce sai ya tuntubi jama’a, kafin ya yanka shawarar neman takara.
Gaya ya gode wa mutanen da su ke yin kiran ya nemi gwamnan jihar Kano a zabe mai zuwa na 2023.
KU KARANTA: Rajistan APC: Oyegun sun raba jiha da Tinubu, Akande
Shugaban kwamitin na harkar zabe a majalisar dattawa, ya ce duk da shekaru biyu kenan da rantsar da su, al’ummar Kano sun yaba da aikin da yake yi.
“Na yi tituna da ayyuka da-dama da su ka ci biliyoyin kudi, wanda mutanen Kano da yawa su ke murna da su.” Gaya ya ke fada wa ‘yan jarida a Abuja jiya.
“Na yi aiki a duka kananan hukumomi 44 da ake da su a jihar Kano. Mazabata ta na da kananan hukumomi 16 ne, amma na kai ayyuka na zuwa ragowar 28.”
“Mutane su na ce mani, idan za ka iya yin wannan a matsayin Sanata, kuma kayi kokari da kayi gwamna, me zai hana ka dawo ka yi takarar gwamna a 2023?”
KU KARANTA: Sanata Kabiru Gaya ya sha ihu a gaban manyan APC a Kano
Ba za ka dauki wannan mataki ba tare da ka tuntubi manya, abokai, masu fada a ji, da malamai a jiha ba.” Sanata Gaya ya ce idan lokaci ya yi, zai dauki mataki.
A makon da ya gabata kun ji cewa Sanata Kabiru Gaya ya fito ya nuna muradinsa na sha'awar ganin mutanen kudu sun fito da shugaban Najeriya a zaben 2023.
Gaya zai mara baya domin ganin shugaban kasa ya fito daga yankin Kudancin kasar nan. A cewarsa, lokaci yayi da ya kamata mutanen Kudu su yi mulki.
A kan lamarin shugabancin kasa kuwa, Sanatan ya na ganin Muhammadu Buhari ya na kokari.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng