Mamaki: APGA ta kayar da manyan jam'iyyu a zaben maye gurbin wakilin mazabar Magama/Rijau
- Jam'iyyar APGA ta bawa jam'iyyar PDP mamaki a zaben maye gurbi da aka gudanar a Jihar Neja
- A ranar Asabar ne hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da sunan Salihu Saleh a matsayin wanda ya lashe zaben maye gurbin
- INEC ta gudanar da zaben ne domin maye gurbin dan mamba mai wakiltar mazabar Magama/Rijau
Jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta samu nasarar lashe zaben maye gurbi na kujerar dan majalisar tarayya na mazabar Magama/Rijau da ke jihar Niger, wanda aka gudanar a ranar Asabar.
Zaben wanda aka ruwaito cewa cike yake da tashe tashen hankula, an bayyana jam'iyyar APGA a matsayin wacce ta lashe zaben, inda ta lallasa jam'iyyar PDP, a sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar.
Ɗan takarar APGA, Salihu Salleh ya samu kuri'u 22,965 inda ya lallasa abokin hamayyar sa Emmanuel Alamu Endoza na jam'iyyar PDP wanda ya samu kuri'u 22,507 da kuma ɗan takarar jam'iyyar ADC, Halilu Yussuf wanda ya samu kuri'u 316.
KARANTA: Rijista: An tashi baran-baran ba shiri bayan rikici ya barke yayin taron shugabannin APC
A cewar takardar sakamakon zaben da aka rabawa manema labarai, gaba daya kuri'un da aka kada a zaɓen guda 46,499, inda halastattun kuri'u suka zamo 45,808, yayin da aka ki amincewa da kuri'u 691.
KARANTA: An kama matasan da ke dillancin hotuna da bidiyon tsiraicin 'yammatan Kano a yanar gizo
Masu kada kuri'a 169,000 ne aka yi wa rejistar zabe a mazabar ta Magama/Rijau a majalisar wakilan tarayya.
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba ta shiga wannan zaben ba, kasancewar kotu ta cire ta daga cikin zaben.
A baya Legit.ng ta rawaito cewa Cif John Odigie-Oyegun, tsohon shugaban jam'iyyar APC, ya ki amincewa da ra'ayin Tinubu da Akande akan sabunta rijista.
Dattijo a APC, Bisi Akande, ya soki aikin sabunta rijistar mambobin jam'iyyar da shugabanci riko a karkashin Mai Mala Buni ke cigaba da gudanarwa.
A yayin da ya ke karbar sabuwar rijitarsa a ranar Asabar, Tinubu ya bayyana cewa yana goyon bayan ra'ayin Akande akan cewa babu bukatar aikin sake sabunta rijistar mambobi.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng