'Yan bindiga sun kashe yara uku a Kaduna, sun yi awon gaba da iyayensu mata

'Yan bindiga sun kashe yara uku a Kaduna, sun yi awon gaba da iyayensu mata

- 'Yan bindiga sun halaka wasu yara yan gida daya su uku a hanyar Kaduna Birnin Gwari

- Sun kuma yi awon gaba da iyayensu mata su biyu da kuma wasu yaran guda hudu

- Gwamnatin jihar Kaduna ta bakin kwamishinan tsaron cikin gida ta tabbatar da faruwar lamarin

Wasu da ake zargin ‘yan fashi ne sun kashe yara uku tare da sace iyayensu mata a kan babbar hanyar Kaduna Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

'Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da wasu yara hudu na wani Muhammadu Gagare, tsohon jami'in cibiyar gyara halaye ta Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ’yan bindigar sun bude wuta a kan matafiya a kusa da Ungwan Dangedda da ke kusa da Buruku, da misalin karfe 11 na safiyar Alhamis.

KU KARANTA KUMA: Rikicin APC a Kwara: An kwantar da jiga-jigan jam’iyyar 5 bayan musayar naushi da jefe-jefen kujeru da suka yi

'Yan bindiga sun kashe yara uku a Kaduna, sun yi awon gaba da iyayensu mata
'Yan bindiga sun kashe yara uku a Kaduna, sun yi awon gaba da iyayensu mata Hoto: @PremiumTimesng
Source: UGC

An rahoto cewa direban motar ya rasa yadda zai yi da motar bayan harsashi ya same shi.

Mahaifin yaran da aka kashe ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa Saidu, daya daga cikin yaran da ya rasa a harin, dalibi ne a Kaduna.

“Ya’yana uku Saidu, Abdulrashid da Rahmatu aka kashe. Yan fashin suka kuma yi awon gaba da wasu yaran nawa su hudu tare da matana biyu duk a rana daya. Ba mu ji daga bakin masu garkuwar ba saboda matana ba sa dauke da wayoyi a lokacin da lamarin ya faru,” inji shi.

Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Gidaje na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa amma ya ce hatsari ne ya faru bayan ‘yan bindigar sun bude wa matafiya wuta.

A cewarsa, “Rahoton tsaro ya nuna cewa‘yan fashin sun far wa matafiya a kan hanya yayin da suke guduwa daga sintirin jami’an tsaro."

Ya ce aikin ceto da aka yi ya nuna cewa mutum shida sun mutu nan take kamar yadda aka ambaci sunayensu a kasa:

“Abdurrashid Ya’u, Sa’idu Ya’u, Ramatu Ya’u , da wani jinjira da ba a gane ko wanene ba. Sauran sune Suwaiba Ali da Sulaiman Ustaz.”

KU KARANTA KUMA: Kano ta amince da naira miliyan 245 domin yin auren mata da yawa

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel