Fasto Adeboye ya yi hasashen lokacin da ta’addanci zai zo karshe a Nigeria
- Fasto Enoch Adeboye ya kaddamar da cewa ta’addanci zai zo karshe kwanan nan a Najeriya
- Malamin addinin ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 5 ga watan Fabrairu, a sansanin Redeemed da ke hanyar babban titin Lagas-Ibadan
- Adeboye ya bayyana cewa yana da yakinin cewa Najeriya za ta rabu da garkuwa da mutane da kashe-kashe kwanan nan
Shugaban cocin Redeemed Christian Church of God, RCCG, Fasto Enoch Adeboye a daren ranar Juma’a, 5 ga watan Fabrairu, ya ce kwanan nan ta’addanci zai zama tarihi a Najeriya.
Da yake magana a wani taron ibada na watan Fabrairu, Adeboye ya ce baya ga Najeriya, dukkanin kasashen duniya za su samu yanci daga ta’addanci.
KU KARANTA KUMA: Dandalin Kannywood: Allah ya yi wa mahaifin shahararren mawaki Ali Jita rasuwa
A cewarsa, duk wani rikici da ke da farko dole ne yayi karshe PM News ta ruwaito.
“Ina iya fadi cike da kwarin gwiwa cewa ko majima ko badade, za a manta da ta’addanci a Najeriya. A sauran kasashen duniya inda yake da akwai yan ta’adda, Ina so ku sanya a ranku, yana da farko, zai yi karshe.”
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Amurka ta goyi bayan Okonjo-Iweala ta jagoranci WTO
A gefe guda, Shahararren malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya nuna tabbacin cewa fashi da makami da garkuwa da mutane za su zama tarihi a jihar Zamfara da arewa.
Gumi ya bayar da tabbacin ne a ranar Litinin, 2 ga watan Fabrairu, a yayinda ya ziyarci jihar Zamfara kan batun tattaunawa da yan bindigar da ke muradin ajiye makamansu.
Malamin ya ce zaman lafiya zai dawo arewa da Naeriya, inda ya kara da cewa ana kokari don samun mafita mai dorewa kan rikicin manoma da makiyaya, TVC News ta ruwaito.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng