A yi amfani da kasafin tsaro wurin shawo kan matsalar 'yan bindiga, Gumi ya shawarci FG

A yi amfani da kasafin tsaro wurin shawo kan matsalar 'yan bindiga, Gumi ya shawarci FG

- Sheikh Ahmad Gumi ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi amfani da kasafin tsaro wurin samar da bukatun Fulani

- Ya ce biliyoyin kudin da ake warewa domin tsaron kasa sun isa har sun yi yawa wurin samar da bukatun Fulani da ke ta'addanci

- Malamin ya kai ziyarar kwana biyar ga Fulani dake dajikan jihar Zamfara wadanda suka addabi yankin da ta'addanci

Babban malami mazaunin jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi amfani da kasafin kudin da ta ware domin yaki da ta'addancin da ke mamaye arewa.

Gumi, wanda ya yi magana a cigaban ziyarar kwana biyar da ya kai wa Fulani a jihar Zamfara, ya ce manyan kudaden da ake warewa wurin tsaron kasar nan kamata yayi a yi amfani da su wurin shawo kan matsalar Fulani.

"Wadannan biliyoyin sun isa har sun yi yawa wurin shawo kan bukatun Fulani wanda ya hada da kayan more rayuwa, horar da su tare da samar musu da jari," ya kara da cewa.

Ya ce da yawa daga cikin Fulanin sun rasa dukiyarsu saboda satar shanu da kuma yadda wasu jami'an tsaro suke tatsarsu, The Punch ta wallafa.

KU KARANTA: Mutum 6 sun sheka lahira, 6 sun jigata bayan hatsarin da 'yan bindiga suka haddasa a titin Birnin Gwari

A yi amfani da kasafin tsaro wurin shawo kan matsalar 'yan bindiga, Gumi ya shawarci FG
A yi amfani da kasafin tsaro wurin shawo kan matsalar 'yan bindiga, Gumi ya shawarci FG. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

Gumi wanda ya zagaya dajin kusa da Daki takwas, ya yi kira ga Fulani da su yada makamansu kuma su kiyaye zubda jini.

Ya tabbatar musu da cewa Gwamna Bello Matawalle ya mayar da hankali kuma zai share musu hawayensu.

Gumi ya yi musu alkawarin cewa zai yi iyakar kokarinsa wurin mika sakonninsu da bukatunsu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A yayin karin bayani, ya ce zai cigaba da tattaunawa da gwamnatin jihar Zamfara domin tabbatar da cewa ba a samu wanda ya karya alkawari ba.

Kafin fara zagayen, Gumi da tawagarsa sun kai wa Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello ziyara a fadarsa inda ya sanar da su wasu daga cikin matsalolin da suke fuskanta daga Fulani.

KU KARANTA: Gwamnonin arewa sun yi magana da kakkausar murya a kan harin da ake kaiwa makiyaya

A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga sun kutsa wata coci inda suka halaka wani mutum mai matsakaicin shekaru mai suna Ken Ekwesianya, matarsa da diyarsu a Azia da ke karamar hukumar ihiala ta jihar Anambra.

Kamar yadda majiya ta tabbatar, wanda aka kashen an halaka shi ne a farfajiyar cocin wurin karfe 7 na yammacin ranar Alhamis, Daily Trust ta wallafa.

Har a halin yanzu babu gamsasshen bayani game da lamarin amma kakakin rundunar 'yan sandan na jihar, Haruna Mohammed, ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce ana cigaba da bincike.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel