Mutum 6 sun sheka lahira, 6 sun jigata bayan hatsarin da 'yan bindiga suka haddasa a titin Birnin Gwari
- Rayukan mutane 6 sun salwanta yayin da wasu 6 suka jigata sakamakon mummunan hatsarin da ya auku a titin Birnin Gwari
- 'Yan bindigan da jami'an tsaro suka biyo ne suka haddasa hatsarin bayan sun budewa ababen hawa wuta
- Harsashi ya samu wani direba daga nan motar ta kwace masa inda ta dinga tintsirawa a kan titin kafin ta tsaya
Mutane shida sun rasu sakamakon hatsarin da 'yan bindiga suka haddasa a kan babban titin Kaduna zuwa Birnin Gwari.
Wasu mutum shida daga cikin wadanda suka yi hatsarin sun samu miyagun raunika.
'Yan bindigan da aka biyo sakamakon sintirin da jami'an tsaro suka tsananta a yankin, sun hau babbar hanyar inda suka dinga harbin ababen hawa da ke wucewa.
An harbi daya wani matukin wata motar haya a yayin da suke ruwan wutar, TVC News ta wallafa.
KU KARANTA: Jami'an tsaro da farin kaya sun cafke Nastura da wasu jiga-jigan CNG a Kaduna
Daga nan ne motar ta kwace masa inda ta dinga juyawa a titi kafin daga bisani ta tsaya.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya ce 'yan bindigan sun tsere daga titin.
Gwamnatin jihar Kaduna ta yi alhinin aukuwar lamarin inda ta yi addu'ar rahama ga mamatan tare da fatan samun sauki ga wadanda suka samu rauni.
KU KARANTA: Bidiyon magidanci ya saki matarsa bayan mahaifiyarta ta hana shi ganin 'ya'yan shi
A wani labari na daban, Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna ya kushe korar da ake wa 'yan kasar nan daga wasu sassan Najeriya inda yace dan Najeriya yana da damar zabar inda yake son zama.
Tsokacinsa na zuwa ne bayan kiran da ake ta yi ga Fulani makiyaya da su bar wasu sassan kasar nan a kan rashin tsaro.
Farko daga cikin wannna bukatar ta fito ne daga gwamnatin jihar Ondo a kan cewa makiyaya su bar dajikan jihar, The Cable ta wallafa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng