'Yan bindiga sun bindige miji, mata da diyarsu a cikin wata coci a Anambra

'Yan bindiga sun bindige miji, mata da diyarsu a cikin wata coci a Anambra

- 'Yan bindiga sun kutsa wata majami'a a jihar Anambra inda suka aika wani mutum, matarsa da diyarsa lahira

- An gano cewa an halaka mutane ukun ne a farfajiyar kotun wurin karfe 7 na yammacin ranar Alhamis

- Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma yace ana bincike

Wasu 'yan bindiga sun kutsa wata coci inda suka halaka wani mutum mai matsakaicin shekaru mai suna Ken Ekwesianya, matarsa da diyarsu a Azia da ke karamar hukumar ihiala ta jihar Anambra.

Kamar yadda majiya ta tabbatar, wanda aka kashen an halaka shi ne a farfajiyar cocin wurin karfe 7 na yammacin ranar Alhamis, Daily Trust ta wallafa.

Har a halin yanzu babu gamsasshen bayani game da lamarin amma kakakin rundunar 'yan sandan na jihar, Haruna Mohammed, ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce ana cigaba da bincike.

KU KARANTA: Jami'an tsaro da farin kaya sun cafke Nastura da wasu jiga-jigan CNG a Kaduna

'Yan bindiga sun bindige miji, mata da diyarsu a cikin wata coci a Anambra
'Yan bindiga sun bindige miji, mata da diyarsu a cikin wata coci a Anambra. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

"Tabbas, ana cigaba da bincike domin bankado yadda lamarin yake kuma ana tsanantawa wurin tabbatar da cewa an damko wadanda suka aikata mugun abun kuma an yi adalcin da ya dace," yace.

KU KARANTA: El-Rufai ya kushe yadda ake fatattakar 'yan Najeriya daga wasu sassan kasar nan

A wani labari na daban, wata gagarumar gobara ta tashi a kasuwar tippe da ke Gwarinpa a Abuja. An gano cewa mutum 6 sun rasa rayukansu yayin da wasu da yawa suka samu raunika a ranar Alhamis.

Gobarar ta fara ne da daya daga cikin shagunan wanda ya shafa wasu a cikin sa'o'i biyu kafin isowar 'yan kwana-kwana.

Wani ganau ya sanar da The Punch cewa masu kashe gobarar basu iso ba sai wurin karfe 2 na dare bayan kasuwar ta shafe da wuta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel