Rikicin makiyaya da manoma: Tinubu ya yi shiru ne saboda baya so ya rasa hulunansa, Sani

Rikicin makiyaya da manoma: Tinubu ya yi shiru ne saboda baya so ya rasa hulunansa, Sani

- Shehu Sani ya caccaki Bola Tinubu a kan ci gaba da yin shiru game da rikicin makiyaya da manoma a kudu maso yamma

- Tsohon dan majalisan ya ce Tinubu na iya rasa “takalma da hulunansa” idan ya goyi bayan wani bangare a rikicin kabilancin da ya kunno kai a Oyo da Ondo

- Ana ta rade-radin cewa Tinubu wanda ya kasance tsohon gwamnan Lagas kuma babban jigon APC yana hararar kujerar shugaban kasa a 2023

Shehu Sani ya yi ba’a ga babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, a kan shiru da yayi game da rikicin Fulani makiyaya da manoma da ya kunno kai a yankin kudu maso yamma.

A wani wallafa da yayi a ranar Laraba, 3 ga watan Fabrairu, tsohon dan majalisan ya ce Tinubu na ci gaba da yin shiru ne a kan rikicin kabilancin da ya kunno kai sakamakon ba makiyaya wa’adin barin gari da aka yi a jihohin Oyo da Ondo saboda baya so ya “rasa hularsa.”

An zargi Fulani makiyaya da aikata laifuka da suka hada da garkuwa da mutane, fashi da makami, kashe-kashen manoma da kuma lalata gonaki a kudu maso yamma.

Rikicin makiyaya da manoma: Tinubu ya yi shiru ne saboda baya so ya rasa hulunansa, Sani
Rikicin makiyaya da manoma: Tinubu ya yi shiru ne saboda baya so ya rasa hulunansa, Sani Hoto: @ShehuSani @AsiwajuTinubu
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Ba za mu bari mutum 1 ya jawo mana rikici ba, Ganduje ya bayyana dalilin haramta wa Sheikh Kabara yin wa’azi

Gwamna Rotimi Akeredolu wanda yayi korafin cewa miyagu a cikin makiyayan na amfani da jeji a matsayin mafakarsu ya basu wa’adin makonni biyu su bar jejin jihar Ondo.

Sani ya ce shirun Tinubu wani yunkuri ne da Jagaban ke yi don kare “huluna da takalmansa.”

“Idan Jagaban ya yi adawa da koran, zai rasa takalmansa; idan Jagaban ya goyi bayan koran, zai rasa hularsa. Ka sanya takunkuminka mai kauri sannan ka kashe wayarka shugabanmu.”

Ana ta rade-radin cewa Tinubu wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Lagas yana hararar kujerar Shugaban kasa a 2023.

Koda dai babu wani jawabi a hukumance game da hakan, bai fito yayi watsi da rade-radin da ke kara yawa ba.

KU KARANTA KUMA: 2023: Malami ya karyata masu cewa fastocin kamfen dinsa na takarar gwamna sun bayyana

A gefe guda, mun ji cewa akalla makiyaya 37 da shanu 5000 da su ka saba doka, su ke kiwo a cikin jeji a jihar Ondo, sun gamu da fushin dakarun tsaro na Amotekun.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa jami’an Ondo State Security Network Agency wanda aka fi sani da Amotekun sun kori makiyayan da ke jeji.

Shugaban Amotekun na jihar Ondo, Adetunji Adeleye, ya tabbatar da cewa mutanensa sun kutsa daji da nufin koro makiyayan da su ka yi taurin-kai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel