Amotekun sun sa Makiyaya 37 da ke da shanu a bayan gari sun bar jejin Jihar Ondo

Amotekun sun sa Makiyaya 37 da ke da shanu a bayan gari sun bar jejin Jihar Ondo

- Jami’an Amotekun sun kori wasu Makiyaya da su ka ki barin jeji a jihar Ondo

- Gwamnatin Ondo ta bukaci duka Makiyaya su fice daga cikin kungurmin daji

- Amotekun sun bi sahu, sun kori duk Makiyayan da su ka ki biyayya ga dokar

Akalla makiyaya 37 da shanu 5000 da su ka saba doka, su ke kiwo a cikin jeji a jihar Ondo, sun gamu da fushin dakarun tsaro na Amotekun.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa jami’an Ondo State Security Network Agency wanda aka fi sani da Amotekun sun kori makiyayan da ke jeji.

Shugaban Amotekun na jihar Ondo, Adetunji Adeleye, ya tabbatar da cewa mutanensa sun kutsa daji da nufin koro makiyayan da su ka yi taurin-kai.

Cif Adetunji Adeleye ya ce wasu daga cikin makiyayan da ke Ondo sun bar jihar salin-alin, sun ce ba za su iya biyayya ga dokar da aka shigo da ita ba.

KU KARANTA: Ohuabunwa ya shiga sahun masu neman takarar Shugaban kasa

“Wasu sun zabi su tafi Osun, Edo, da Kogi. Mutanenmu sun yi masu rakiya zuwa kan iyaka domin tabbatar da cewa ba su taba gonaki kan hanyar tafiya ba.”

Da yake jawabi, Adeleye ya ce: “Mafi yawan makiyayan sun zo mana ne ta shugabansu, kuma mai ba gwamna shawara a kan harkokin da su ka fi Hausawa.

Jami’an na Amotekun sun yi ram da makiyayan ne a jejin Ala, Oda da jejin Ofosu.

“An kama makiyaya 37 dauke da shanu 5000.”

KU KARANTA: Rikicin Makiyaya: An hallaka Fulani da shanu a danyun hare-hare

Amotekun sun sa Makiyaya 37 da ke da shanu a bayan gari sun bar jejin Jihar Ondo
Gwamna Akeredolu na Jihar Ondo Hoto: www.thenationonlineng.net
Asali: UGC

“Za mu mika masu laifin ga shugaba ya fitar da su, daga nan duk wanda aka sake kama wa zai shiga hannu, kuma za a gurfanar da shi." Inji Adeleye.

Hakan na zuwa ne bayan gwamna Rotimi Akeredolu ya bada umarnin cewa duk makiyayan da su ka tare a kungurmin jejin jihar Ondo, su fito.

Gwamnatin Ondo ta ba makiya umarnin su yi rajista da hukuma, ko su tattara su canza mazauni.

Duk da dokar da gwamna Rotimi Akeredolu ya kawo, wasu makiyayan sun ki barin cikin jeji, wannan ya sa jami’an tsaro, su ka shiga su ka tsefe su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng