An kama wasu mutane huɗu da laifin noman tabar wiwi a jihar Ondo

An kama wasu mutane huɗu da laifin noman tabar wiwi a jihar Ondo

- Wasu jami'ai a jihar Ondo sun samu nasarar kame wasu masu noman tabar wiwi a daji

- Ma'aikatar albarkatun kasa ta jihar ta bayyana hakan a matsayin laifi da cin zarafin dajin

- Ma'aikatar ta tabbatar da cewa za a gurfanar da wadanda aka kaman a gaban kotu

Jami'an hadin gwiwa na ma'aikatar Albarkatun Kasa ta jihar Ondo sun kama mutane hudu da laifin noman tabar wiwi a cikin dajin Akure, The Nation ta ruwaito.

An kama su ne saboda lalata bishiyoyin tattalin arziki da nufin dasa itacen tabar wiwi.

Daraktan rundunar hadin gwiwa a ma’aikatar, Alhaji Moshood Obadun, ya ce an cafke wadanda ake zargin ne bayan da suka yi bayani.

KU KARANTA: Daga kara masa wa'adi, IGP Adamu ya karawa wasu jami'ai girma

An kama wasu mutane huɗu da laifin noman tabar wiwi
An kama wasu mutane huɗu da laifin noman tabar wiwi Hoto: The Sun News
Source: UGC

Kwamishinan kula da albarkatun kasa na Ondo, Mista Idowu Otetubi, a nasa bangaren, ya ce za a cafke masu yin zagon kasa a gandun dajin gwamnati da ke fadin jihar.

Ya ce masu yi wa dokar zagon kasa sun yi fatali da umarnin gwamnati da ke cewa duk masu zama ba kan ka'ida ba su bar gandun dajin a fadin jihar.

Kwamishinan, wanda ya ba da tabbacin cewa za a gurfanar da wadanda aka kama a gaban kotu, ya ce akwai ka'idojin aiki wajen aiwatar da duk wani aiki a gandun dajin.

KU KARANTA: Kiran dukkan makiyaya da sunan ‘makasa’ na iya haddasa yaki a kasar nan, in ji El-Rufai

A wani labarin, Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ta ce wasu da aka gargame su 18 ne suka kammala karatun digiri daga jami'ar karatu daga gida ta National Open University ta Najeriya, BBC Hausa ta ruwaito.

A wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar, Francis Enabore ya fitar a yau Alhamis ta ce tsararrun sun kammala jami'ar ne a fannonin karatu daban-daban.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel