Jami'an tsaro da farin kaya sun cafke Nastura da wasu jiga-jigan CNG a Kaduna
- Wasu da ake zargin jami'an tsaro na farin kaya (DSS) sun kama wasu shugabannin CNG a Kaduna.
- Wadanda aka kama sune shugaban kungiyar, Ashir Shariff Nastura da kuma Balarabe Rufai, mai tsarawa na kasa
- Duk da dai ba a bayyana dalilin kama su ba, amma har yanzu an rasa hanyar da za a bi a gano inda suke, wayoyinsu basu shiga
Wasu da ake zargin jami'an tsaro na farin kaya ne sun kama wasu shugabannin CNG a Kaduna. Hakan ya faru ne bayan an dakatar da wani taro da kungiyar zata yi babu dadewa.
Wadanda aka kama sune shugaban BOT, Ashir Sheriff Nastura da kuma NC na kungiyar, Balarabe Rufai, The Nation ta wallafa.
Kakakin kungiyar, Abdul-Azeez Suleiman ya sanar da manema labarai cewa har yanzu ba a san dalilin kama su ba don an kasa gano hanyar da za a bisu kuma wayoyinsu basu shiga.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An tsinto rubabbiyar gawar yariman da aka yi garkuwa da shi
Idan ba a manta ba, a ranar Laraba DSS ta kara jan kunnen mutanen da suke yunkurin kawo cikas ga zaman lafiyar kasa ta hanyar tayar da fadan addini ko na kabila a kasar nan.
Dama manyan kungiyoyin addini na Kasarnan kamar NSCIA, da CAN sun umarci DSS da ta daina zarginsu ta mayar da hankali ga masu tayar da tarzoma.
Duk da CNG bata sanar da jama'a ba, amma kungiyar ta shirya wani taro a ranar Laraba da daddare a NAF dake Kaduna amma ta mayar da taron zuwa ranar Alhamis 11:00am.
CNG ta shirya taron ne don tasan yadda za ta bullo wa rikicin fatattakar Fulani daga kudancin Najeriya.
KU KARANTA: 2023: APC ta musanta rade-radin goyon bayan Goodluck Jonathan
A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga sun kwace N20,000,000 daga hannun akawun ofishin gwamnan jihar Ekiti a ranar Laraba a wani hari da suka kai, The Nation ta wallafa.
Sun kai musu harin ne suna hanyar dawowa daga wani banki wuraren titin ofishin gwamnati dake Ado-Ekiti inda suke ciro kudaden.
Ganau sun tabbatar da yadda 'yan bindigan suka yi ta harbe-harbe kafin su kwace kudaden daga hannunsu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng