Bidiyon magidanci ya saki matarsa bayan mahaifiyarta ta hana shi ganin 'ya'yan shi

Bidiyon magidanci ya saki matarsa bayan mahaifiyarta ta hana shi ganin 'ya'yan shi

- Wani dan Najeriya ya rabu da matarsa saboda mahaifiyarta ta hana shi ganin yaransa

- An ga bidiyon wani mutum a fusace yana kwashe kayansa yana ce wa matarsa zamansu ya kare

- Ya bayyana takaicinsa akan yadda sirikarsa ta hana shi ganin yaransa saboda tayi ikirarin bai gaisheta ba

Wani dan Najeriya ya rabu da matarsa bayan mahaifiyarta ta hana shi ganin yaransa saboda ikirarin bai gaisheta ba.

A wani bidiyo wanda mijin yayi, an gan shi yana kwashe kayansa yana sanar da matarsa cewa zamansu ya kare saboda mahaifiyarta ta hana shi ganin yaransa.

Ya bayyana yadda mahaifiyarta tayi ikirarin cewa ya shiga gidanta ba tare da ya gaisheta ba, The Nation ta wallafa.

Bidiyon magidanci ya saki matarsa bayan mahaifiyarta ta hana shi ganin 'ya'yan shi
Bidiyon magidanci ya saki matarsa bayan mahaifiyarta ta hana shi ganin 'ya'yan shi. Hoto daga @Thenation
Source: Twitter

KU KARANTA: Hoton dankareriyar motar miliyoyin naira da Emmanuella ta siya ya janyo cece-kuce

Matar ta bukaci yayi hakuri kada ya kawo karshen tarayyarsu saboda al'amari ne wanda za su iya zama su tattauna akai don a kawo maslaha.

Saidai mijin ya yi kunnen uwar shegu da rokon matar, inda yace ya hakura da auren.

KU KARANTA: Yara 2 sun sheka lahira, mahaifiyarsu ta jigata bayan shan maganin gargajiya a Kano

A wani labari na daban, wasu yara 2, Maryam Abubakar da Abdulkadir Abubakar sun rasa rayukansu bayan sun sha wani tsumi da mai maganin gargajiya ya basu.

Mahaifiyarsu, Sadiya Abubakar, yanzu haka bata san inda kanta yake ba, likitoci suna iyakar kokarin ganin sun ceto rayuwarta a asibiti.

Al'amarin ya faru ne a ranar Talata a Kwarin Barke dake Sabuwar Gandu a karamar hukumar Kumbotso dake jihar Kano, Daily Trust ta wallafa.

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar, DSP Abdullahi Kiyawa ya ce bayan 'yan sanda sun yi bincike ne suka ga wata gora cike da wani maganin gargajiya da wata gorar koko a gefen gawawwakin a dakin da aka same su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel