Tinubu ba zai ga ko kofar fadar shugaban kasa ba a 2023, in ji Wike
- Gwamna Nyesom Wike ya nuna kokwanto a kan kudirin shugabancin Bola Tinubu
- Gwamnan jihar Rivers ya nuna karfin gwiwar cewa APC za ta sha mamaki a zaben 2023
- Kudirin shugabancin Tinubu na ta samun gagarumin masauki a kafofin watsa labarai
Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya bukaci babban jigon jam’iyyar All Progressive Congress (APC), Bola Tinubu, da ya fuskanci wasu abubuwa masu amfani, inda ya bayyana cewa jam’iyyarsa da shi kansa ba za su ji kamshi shugabanci ba a zaben 2023.
Wike, ya baiwa Tinubu shawarar a ranar Alhamis, a Yola babbar birnin jihar Adamawa yayinda yake rangadi na wani aiki da Gwamna Ahmadu Fintiri ya aiwatar.
Ya ce da wadannan gagarumin kokari da gwamnonin Peoples Democratic Party (PDP) suka yi da kuma gazawar APC karkashin gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, yan Najeriya ba za su sake kuskuren zabar wata jam’iyya mara alkibla ba.
KU KARANTA KUMA: Saurayi ya maka budurwa kotu bayan tura mata N5K amma taƙi zuwa ɗakinsa
“Da wannan abunda na gani a yau a Adamawa, ina al’ajabin yadda mutum mai hankali zai ki sake zabar PDP a jihar. Abunda ke faruwa a jihar Adamawa maimaicin abunda ke faruwa ne a sauran jihohin PDP.
“Da gagarumin ci gaban da ke gudana a jihohin PDP da tarin rashawa da ke gudana a karkashin gwamnatin APC, ba sabon labari bane cewa PDP ta kama hanyar fatattakar masu mamaya da kuma kwato gidanta da kai yan Najeriya zuwa inda take muradin zuwa,” in ji shi.
Gwamnan na Rivers, wanda ya yaba da matsayin Najeriya a rahoton Transparency International (TI) kan rashawa, ya ce shuggabancin APC mai ci tana maraba tare da kare barayin mutane.
“A yau, Wike na iya kasancewa gwamna mafi rashawa, amma da zaran na koma APC da PDP, na zama tsarkakke. Hakan na nufin APC idan barayin mutane ne. Wadannan ba kalamai na bane, kawai ina maimaita abunda tsohon Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole ya fadi ne. Yan Najeriya na da ilimi, ba za su sake shiga jirgin ruwan da ya kife da su ba,” in ji shi.
KU KARANTA KUMA: Hukumar yan sanda ta sanar da kyautar N10m ga duk mutumin da ya iya bayyana inda wasu masu laifi suke
Wike ya bayyana cewa Najeriya bata taba rabuwa ba kamar yadda ta fuskanta a karkashin gwamnatin APC sannan cewa rashin tsaro ya zama babban masana’anta a karkashin shugaba Buhari, jaridar The Guardian ta ruwaito.
Ya shawarci Shugabannin APC da su koma jihar Adamawa sannan su koyi yadda ake bunkasa mutane ta ayyuka, cewa shugaba Buhari na iya tabatar da ci gaban da Gwamna Fintiri ya kawo.
A gefe guda, Gwamnan jihar Ribas ya bayyana cewa 'yan Najeriya basu girbi alherin da suke tsammani a zabar APC ba.
Ya ce babban kuskure 'yan Najeriya suka yi da suka zabi jam'iyyar APC domin ta mulke su.
Gwamnan ya bayyana cewa yakamata 'yan Najeriya yanzu kam su hankalta su zabi jam'iyyar PDP
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng