Hukumar yan sanda ta sanar da kyautar N10m ga duk mutumin da ya iya bayyana inda wasu masu laifi suke

Hukumar yan sanda ta sanar da kyautar N10m ga duk mutumin da ya iya bayyana inda wasu masu laifi suke

- Rundunar yan sandan Najeriya na neman taimakon al’umman kasar a binciken wani laifi da take yi

- Hukumar yan sandan ta saki wani jawabi kan wasu mutane da take nema ruwa a jallo kan aikata wani laifi

- Hukumar bata bayyana inda aka aiwatar da laifin ba

Yan Najeriya a shafin Twitter sun yi martani a kan wata wallafa da rundunar yan sanda tayi inda ta sanar da bayar da kyautar kudi naira miliyan 10 ga duk wanda ya kawo jawabai masu amfani kan inda wasu masu laifi da aka hasko a kamarar CCTV suke.

An wallafa rubutun ne a shafin Twitter na rundunar sojin Najeriya a ranar Alhamis, 4 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Sheikh Kabara: Ganduje ya hana mun yin wa’azi saboda na yi adawa da tazarcen shi

Hukumar yan sanda ta sanar da kyautar N10m a duk mutumin da ya iya bayyana inda wasu masu laifi suke
Hukumar yan sanda ta sanar da kyautar N10m a duk mutumin da ya iya bayyana inda wasu masu laifi suke Hoto: @PoliceNG, The Nation
Source: UGC

Rubutun na dauke da hotunan wasu masu laifi biyu da kamarar CCTV ta dauke su a wajen da suka aikata laifin.

A cewar yan sandan, al’umman kasar da ke muradin bayar da rahoto kan lamarin na iya ziyartan ofishin yan sanda mafi kusa don yin hakan.

Hukumar yan sandan ta kuma ce yan Najeriya da ke da ikon kama masu laifin na iya aikata hakan sannan su mika su ga ofishin yan sanda mafi kusa.

Hukumar ta kuma bayyana lambobin wayar da yan kasar za su iya kira don bayar da bayani.

KU KARANTA KUMA: Ko shakka babu yan Najeriya za su sake zabar APC a 2023, in ji Hope Uzodinma

Sai dai, wasu yan kasar wadanda suka yi martani ga lamarin sun tambayi dalilin da yasa yan sandan ba za su iya amfani da bayanan kimiyar lissafi wajen gano masu laifin ba.

@VictorIsrael_ ya ce:

“An dauki bayanai da hotunanmu a lokacin yin rijistan katin zabe, lasisin tuki, NIN, JAMB da BVN. Ku dauki wadannan hotunan, ku nemi hotunan da yayi daidai da wadannan sannan ku neme su sai ku raba naira miliyan 10 da babu shi a tsakaninku sannan abu mafi muhimmanci ku siya sabbin motoci!”

@layilawal1 ya ce:

“Kuna da dukkan bayananmu, bvn, zanen yatsa, hoton fasfot, sannan kuma kuke bayar da naira miliyan 10 ga al’umma don su nemo mutanen da hotonsu ma bai nuna da kyau ba.”

@Hustle40592932 ya rubuta:

''Ni na ma san mutumin, amma kafin na fada ma kowa, sai kun fara bani rabin kudin wanda shine 5m.”

Christopher Sunny @ituma2496 ya ce:

“Ku biya rabin kudin 5m sai ku cika sauran idan aka kammala aiki. Idan kun amince da hakan sai mu fara aikin bincike daga yanzu. Mutum na karshe dazan yarda dashi wajen yin kasuwanci ita ce rundunar yan sandan Najeriya. Wayoo ne inkiyarsu.”

A wani labarin kuma, jaruman mutanen gari sun dakile harin da yan bindiga suka yi niyyar kai wa rugar Maikudi da ke mazabar Kerawa a karamar hukumar Igabi na jihar Kaduna.

Yan bindigan sun taho da niyyar garkuwa da mutane amma dole yasa suka tsere sakamakon yadda mutanen garin suka yi fito na fito da su, Vanguard ta ruwaito.

Samuel Aruwan, kwamishinan ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida na jihar kaduna, ya ce yan banga na garin sun hada kai sun dakile harin, kuma sun ci galaba kansu yayin musayar wuta hakan yasa yan bindigan suka tsere.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel