Jaruman mutanen gari sun fattaki 'yan bindiga a rugar makiyaya a Kaduna

Jaruman mutanen gari sun fattaki 'yan bindiga a rugar makiyaya a Kaduna

- Mutanen gari sun dakile harin da yan bindiga suka yi yunkurin kai wa rugarsu a Kaduna

- Yan bindigan sun zo garin da nufin garkuwa da mutane ne amma yan bangar garin suka fatattake su

- Sai dai mutum daya ya riga mu gidan gaskiya sannan dan uwansa ya jikkata sakamakon artabun da yan bindigan

Jaruman mutanen gari sun dakile harin da yan bindiga suka yi niyyar kai wa rugar Maikudi da ke mazabar Kerawa a karamar hukumar Igabi na jihar Kaduna.

Yan bindigan sun taho da niyyar garkuwa da mutane amma dole yasa suka tsere sakamakon yadda mutanen garin suka yi fito na fito da su, Vanguard ta ruwaito.

Jaruman mutanen gari sun fattaki 'yan bindiga a rugar makiyaya a Kaduna
Jaruman mutanen gari sun fattaki 'yan bindiga a rugar makiyaya a Kaduna. Hoto: @channelstv
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Zalunta ta gwamnatin Kano ta yi, Sheikh Abduljabbar Kabara

Samuel Aruwan, kwamishinan ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida na jihar kaduna, ya ce yan banga na garin sun hada kai sun dakile harin, kuma sun ci galaba kansu yayin musayar wuta hakan yasa yan bindigan suka tsere.

Sai dai wani mazaunin garin, Alhaji Maikudi Husaini ya riga mu gidan gaskiya sakamakon artabun. Dan uwansa, Nafiu Husaini shima ya samu rauni kuma yana asibiti yana karbar magani.

KU KARANTA: Allah ya yi wa kawun Sheikh Isa Ali Pantami rasuwa

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar ya yi bakin cikin samun labarin inda ya yi addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu yayin da ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalansu.

Jami'an tsaro za su cigaba da sintiri a yankunan domin tabbatar da tsaro.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel