Sunayensu: Hameed Ali ya nada DCGs 2, ACGs 5, ya sauya wa manyan jami'ai 5 wurin aiki

Sunayensu: Hameed Ali ya nada DCGs 2, ACGs 5, ya sauya wa manyan jami'ai 5 wurin aiki

- Hameed Ali, shugaban hukumar kwastam, ya karawa wasu jami'ai girma tare da yi wa wasu sauyin wurin aiki

- Daga cikin wadanda aka karawa girma akwai mutane biyu da aka nada a matsayin DCG da wasu biyar a matsayin ACG

- Kakakin Kwastam ya rawaito cewa Hameed Ali ya ce karawa jami'ai girma da kuma sauyawa wasu wurin aiki yana daga cikin kara karfafa aikin hukumar

Shugaban hukumar hana fasa kwauri ta kasa wacce aka fi sani da 'Kwastam', Hameed Ali, ya karawa wasu manyan ma'aikata mukami.

Daga cikin sabbin karin matsayin da ya yi a hukumar kwastam, Hameed Ali ya nada manyan mataimakansa (DCG) guda biyu, kananan mataimaka (ACG) guda biyar.

Kazalika, shugaban na hukumar ta kwastam ya sauyawa wasu manyan jami'an kwastam guda biyar wurin aiki.

Kakakin rundunar hukumar Kwastam na kasa, Joseph Attah, ne ya sanar da hakan ranar Alhamis.

A cikin sanarwar da Attah ya fitar, ya ce an nada Abdullahi Babani da Mohammed Boyi a matsayin DCG a bangarori daban-daban.

DUBA WANNAN: Wahalar man fetur ta tunkaro Abuja da sauran jihohin arewa gadan-gadan

Ya kara da cewa an nada sabbin ACG guda biyar da suka hada da; Saidu Galadima da Uba Mohammed.

Sauran sune; Hamza Gummi, Usman Dakingari, da kuma SM Modibbo.

A cewar Attah, Hameed Ali, ya sauyawa wasu manyan jami'an hukumar Kwastam guda biyar wurin aiki.

Sunayensu: Hameed Ali ya nada DCGs 2, ACGs 5, ya sauya wa manyan jami'ai 5 wurin aiki
Hameed Ali
Asali: UGC

Wadanda sauyin wurin aikin ya shafa sun hada da DCG David Chikan wanda aka sauya daga TRADOC zuwa FATS.

An sauyawa Comptroller Mohammed Auwal wurin aiki daga PHI zuwa PHII a yayin da aka mayar da Comptroller Yusuf Garba zuwa PHI daga Kebbi.

DUBA WANNAN: FG ta fitar da muhimmiyar sanarwa ga dukkan masu amfani da bankuna a Najeriya

A cewar Attah, Comptroller Hafiz Kalla zai tashi daga FATS ya koma Kebbi yayin da Comptroller Bello Jibo zai bar shiyyar Bauchi/Gombe ya koma iyakar Najeriya da kasar Benin, wacce aka fi sani 'Seme' boda.

Attah ya rawaito cewa Hameed Ali ya bayyana cewa karin girma da sauyawa jami'ai wurin aiki yana daga cikin kokarinsa na kawo gyara tare da inganta aikin hukumar Kwastam.

(NAN)

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel