Yaki da ta’addanci: El-Rufai ya ce sabbin shugabannin tsaro za su yi nasara

Yaki da ta’addanci: El-Rufai ya ce sabbin shugabannin tsaro za su yi nasara

- Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi martani ga matsalolin tsaro a kasar

- Dan siyasan ya yi maraba da nadin sabbin shugabannin tsaro

- El-Rufai ya yi karin haske kan yadda kwamandojin soji za su iya nasara kan rashin tsaro a kasar

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya nuna karfin gwiwar cewa sabbin shugabannin tsaro a kasar za su iya yaki da rashin tsaro da sauran laifuffuka.

El-Rufai ya ce yana sa ran sabbin kwamandojin soji za su yi nasara saboda za su shigo da sabon karfi, a cewar jaridar This Day.

KU KARANTA KUMA: 2023: Dinkewar Yari da Marafa ba barazana bace a gare mu, PDP tayi martani

Yaki da ta’addanci: El-Rufai ya ce sabbin shugabannin tsaro za su yi nasara
Yaki da ta’addanci: El-Rufai ya ce sabbin shugabannin tsaro za su yi nasara Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

An tattaro cewa ya yi jawabin ne a lokacin da ya zanta da manema labarai a yayin ziyarar da ya kai wa gwamnan jihar Niger, Abubakar Sani Bello, a Minna a yammacin ranar Talata, 2 ga watan Fabrairu.

Gwamnan ya ce:

“A duk lokacin da aka samu sabbin mutane, suna zuwa ne da sabon karfi da kuma hangen kawo sauyi. Saboda haka, muna fatan abubuwa za su inganta.”

El-Rufai ya bayyana cewa shi da takwaransa na jihar Niger sun gabatar da abunda suke ganin shine mafita ga ayyukan ta’addanci a jihohinsu na fiye da shekaru biyu da rabi.

KU KARANTA KUMA: Korona: Ku yi allurar rigakafi ko ku mutu, FG ta gargadi yan Nigeria

Ya shawarci kwamandojin soji da su yi nazarin rahotannin da aka gabatarwa da shugabannin tsaron da suka gabata wanda a ciki aka bayar da shawarwari kan yadda za a duba annobar rashin tsaro a kasar.

A wani labari na daban, mun ji cewa hukumar tsaro ta farin kaya ta gargadi 'yan Najeriya kan shirin da wasu suke yi na tada hankali.

Hukumar ta ce akwai wasu mutane da kungiyoyi da suke shirin tayar da kayan baya.

Akwai yiyuwar tada rikici da hare-hare a wuraren ibada da wurare masu muhimmaci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel