Katsina: 'Yan sanda sun sheke 'yan bindiga uku yayin musayar wuta

Katsina: 'Yan sanda sun sheke 'yan bindiga uku yayin musayar wuta

- A kalla 'yan bindiga uku ne suka bakunci lahira yayin wata musayar wuta da 'yan sanda a jihar Katsina

- An yi musayar wuta a tsakanin 'yan bindiga da jami'an 'yan sanda a daren ranar Talata a yankin karamar hukumar Danmusa

- Jami'an rundunar 'yan sanda sun yi wa maharan kwanton bauna tare da tarfasu a tsakanin wasu kauyuka

A ƙalla mahara uku yan sanda suka aika lahira cikin daren Talata a ƙaramar hukumar Ɗanmusa dake jihar Katsina.

Maharan waɗanda adadinsu ya haura hamsin, sun kutsa ƙauyukan Unguwar Ɓera da Tasha Mangoro cikin wannan daren, daga bisani mazauna ƙauyukan suka nemi agaji daga jami'an tsaro.

Tawagar jami'an rundunar 'yan sanda ta kaddamar da harin kwanton bauna tare da tarfa tawagar 'yan bindigar a wani wuri da ke tsakanin kauyukan Mara da Tashar Gajere

Bayan karɓar kiran wayar ne, nan take kwamandan yan sanda na yankin shi da tawagarsa su ka yi musu kwantan ɓauna tsakanin Mara da Tashar Gajere, kamar yadda Punch ta rawaito.

Katsina: 'Yan sanda sun sheke 'yan bindiga uku yayin musayar wuta
Katsina: 'Yan sanda sun sheke 'yan bindiga uku yayin musayar wuta
Asali: UGC

Rahotanni sun ce, maharan sun mayar da martani lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar uku daga cikin maharan.

Kwamishinan 'yan sanda na Katsina, Sanusi Buba, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya kara da cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na dare.

Ya kuma bayyana cewa an kwato sabbin AK 47 guda biyu tare da harsasai masu rai guda 7.62 daga hannun yan fashin.

Sai da kuma ‌kwamishinan ya yi musu albishir da cewa har yanzu kofar tattaunawa a buɗe ta ke ga duk wani dan ta'adda da ya tuba, yana mai gargadin cewa gwamnati za ta ci gaba da yin maganin matattun' yan ta'addan.

A baya bayan nan ne Legit.ng ta rawaito cewa An yi musayar wuta tsakanin 'yan bindiga da dakarun rundunar soji a kananan hukumomin jihar Katsina guda biyu.

A yayin dukkan musayar wutar, dakarun rundunar soji sun kashe 'yan bindiga biyar.

A cewar Birgediya Janar Benard Onyeuko, rundunar soji ta kam wasu mutane uku da ke taimakon 'yan bindiga da bayanan sirri.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel