Wasu 'yan bindiga sun kashe wasu mazauna Kaduna a sabbin hare-hare

Wasu 'yan bindiga sun kashe wasu mazauna Kaduna a sabbin hare-hare

- Wasu 'yan bindiga sun kai hari wani yankin Lere da ke jihar Kaduna a Najeriya

- 'Yan bindigan sun hari kauyen, tare da bude wuta ba kakkautawa kan wasu mutane

- Sun kuma kashe wasu adadin mutane tare da raunata wasu yayin da wasu suka tsere

Wasu ‘yan bindiga guda shida sanye da abin rufe fuska da kuma bakaken kaya sun mamaye Warsa Piti, a Gundumar Mariri da ke karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna suka kashe mutane biyu a ranar Litinin, The Punch ta ruwaito.

An ce 'yan bindigar sun yi harbi ba kakkautawa, inda suka kashe mutanen kauyen biyu kafin su tsere zuwa cikin dajin lokacin da jami'an soji suka isa yankin.

Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Mista Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwan haka.

Ya ce, “Sojoji karkashin inuwar Operation Safe Haven sun ba da rahoton wani hari da 'yan fashi suka kai a Warsa Piti, a Gundumar Mariri da ke Karamar Hukumar Lere.

KU KARANTA: Hanya mafi sauki don magance rikicin makiyaya, Mataimakin gwamnan Benue

Wasu 'yan bindiga sun kashe wasu mazauna Kaduna a sabbin hare-hare
Wasu 'yan bindiga sun kashe wasu mazauna Kaduna a sabbin hare-hare Hoto: The Sun News
Asali: UGC

“Sojojin da suka samu kiran wayar gaggawa sun tattara zuwa wurin inda suka yi artabu da maharan sannan suka gudu zuwa daji. Duk da haka, an riga an kashe mutum biyu, waɗanda aka ambata da suna Sale Muhammad da Aguno Bawuro.

Gwamnati ta bada rahoton cewa an kai wani harin a Randagi da ke karamar hukumar Birnin Gwari yayin da aka kashe wani mutum.

“A wani lamarin na daban, sojojin sun kuma bayar da rahoton cewa wasu matasa da ba a san ko su wanene ba sun kai hari a wani matsugunin makiyaya a kauyen Kurmin Bi na karamar hukumar Zangon Kataf .

“A cewar rahoton, harin ramuwar gayya ce kawai ga harin da aka kai wa Wawan Rafi.

“Makiyayan da ke yankin sun tsere amma maharan sun kashe shanu shida, tare da jikkata wasu hudu. Wani gida ma an kone shi kurmus."

Ya ce gwamna Nasir El-Rufai ya nuna damuwa kan sabbin hare-haren.

Ya kara da cewa "ana ci gaba da bincike kan abubuwan da suka faru, yayin da sojoji ke kara sintiri a sassan yankin," in ji shi.

KU KARANTA: Kwalejin kimiyya da fasaha na Adamawa za ta fara karatun digiri, in ji Rector

A wani labarin, 'Yan sanda a Abuja a ranar Talata, sun tabbatar da sace Mista John Makama, mahaifin Shugaban Karamar Hukumar Bwari, John Gabaya, The Nation ta ruwaito.

CSP Biodun Makanjuola, jami’in ‘yan sanda na shiyya (DPO), mai kula da ofishin 'yan sanda na Bwari, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel